Sakamakon mutuwar mutane 37 wadanda ake zaton masu hakar ma’adanai da suke tsare a hannun hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence; Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya sanar da kafa kwamitin bincike kan wannan muhimmin al’amari.
Gwamnan ya kuma dakatar da kwamandan hukumar NSCDC na jihar da tawagar jami’an da ke aiki tare da shi, domin gudanar da bincike kan lamarin cikin adalci.
A wata sanarwa da ya fitar kuma ya karanta a daren Alhamis, gwamnan ya bayyana mutuwar mutanen a matsayin abin takaici.
Ya kuma ayyana zaman makoki na kwanaki uku tare da dakatar da yakin neman zaɓensa sakamakon mutuwar matasan.
Me ya faru?
Hukumar NSCDC ta ce jami’anta sun kama mutanen ne a ranakun Talata da Laraba a wasu sassan jihar Neja, bisa zargin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
An ce an kama su ne a kusa da Borgu, wani yanki da ake gudanar da ayyukan haƙar ma’adanai.
Sai dai hukumar ta ce mutanen sun rasu ne a ranar Alhamis yayin da suke tsare.
Da farko, jami’an sun yi zargin cewa wata cuta ce ta yi sanadin mutuwarsu.
Rahotanni, sai dai, sun nuna cewa akwai yiwuwar cunkoso da ƙarancin iska a wurin da ake tsare da su ne suka haddasa mutuwar, ko kuma suka taimaka wajen faruwar lamarin.
An kai gawarwakin zuwa babban asibitin Minna domin gudanar da bincike.
Yadda muka samu labari – Iyaye
Mahaifin ɗaya daga cikin mutanen ya shaida wa BBC cewa sun fara neman ƴaƴansu ne bayan sun samu labarin an kama su.
Ya ce an kai ziyara wajen da ake tsare da su bayan kwana uku, amma aka ce ba za a sake su ba.
“Ranar farko mun je, aka faɗa mana cewa mu dawo washegari. Da muka koma aka faɗa mana ba za a sake su, sai washegari. A ranar kuma matata ce ta riga ni komawa, sai ta kira ta ce yara fa sun mutu.”
Mahaifin ya ce hakan ya sa ya ruga zuwa ofishin ƴansandan domin su gane wa kansu abin da ke faruwa, amma aka hana shi shiga.
Sai dai daga baya, lokacin da aka saki gawarwakin, ya je domin duba gawar ɗansa, amma bai same shi ba.
Daga baya ne ya gano cewa ɗansa, Salim, yana raye kuma ya koma gida.
Shi ma wani mahaifi da yaransa ya rasu mai suna da Malam Abdullahi da zanta da jaridar Daily Trust, ya ce da ya je hedkwatar hukumar, an buƙaci ya biya naira 500,000 ne a matsayin kuɗin beli kafin a saki ɗan nasa.
Ya bayyana cewa ɗansa ba ɓarawo ba ne, kuma yana aikin haƙar zinare ne saboda babu wani aikin da zai yi.
“Kuma da ɗan abin da yake samu ne yake taimakonmu a gida. Ko a daren jiya mun kai masa abinci a wajen da ake tsare su. Da safiyar yau muka je kai masa abinci kawai muka samu labarin ya mutu.”
Ɓarkewar zanga-zanga
A wani labarin daban, zanga-zanga ce ta ɓarke a jihar Neja ɗin, inda matasa suka fito suna nuna rashin jin daɗinsu kan mutuwar matasan.
Wani mazaunin Unguwar Tunga Sabon Titi inda lamarin ya faru, wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa matasan da suka fusata sun yi ta jefe-jefe yayin da ƴansanda kuma ke harbi.
A cewarsa, ƴansanda sun harbi mutum huɗu kuma a cikinsu mutum guda ya mutu nan take.
Da farko, jami’ai sun yi zargin cewa wata cuta ce ta yi sanadin mutuwar matasa da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
Tuni dai gwamnatin jihar ta Neja ta sanar da kafa kwamitin bincike don gano musabbabin mutuwar matasan
Lamarin ya sa gwamna Mohammed Umar Bago ayyana makokin kwanaki uku tare da dakatar da yaƙin neman zaɓensa.
Martanin Civil Defence
Da take jawabi kan lamarin, hukumar tsaron ta ƙasa ta tabbatar da mutuwar mutane, waɗanda ta ce jami’anta sun kama bisa zargin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, bayan wani samame da jami’an hukumar suka gudanar a wasu sassan Jihar Neja a ranakun 15 da 16 ga Satumbar 2026.
Hukumar ta ce an kama mutanen ne a wani samame na haɗin gwiwa da rundunar NSCDC ta Jihar Neja ta gudanar a yankunan M.I. Wushishi da Lukoto, a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin kasa na daƙile hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da kuma kare albarkatun ƙasa.
Biyo bayan rahotannin mutuwar waɗanda ake zargin, Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, OFR, mni, ya ba da umarnin kafa wani babban kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin mataimakin kwamandan janar mai kula da harkokin leƙen asiri da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.
NSCDC ta kuma ce tana aiki tare da hukumomin lafiya da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da daukar matakan da suka dace na kiwon lafiya da kare lafiyar jama’a.
Hukumar ta yi ƙarin haske cewa rahotannin da ke alaƙanta mutuwar da wata cuta a matsayin mara tushe, “domin har yanzu ana jiran sakamakon gwaje-gwajen likitoci da na dakin gwaje-gwaje kafin a tabbatar da musabbabin mutuwar.”
Gwamnati ta dakatar da shugaban NSCDC na Neja
Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin dakatar da shugaba hukumar tabbatar da tsaro da kare haƙƙin al’umma, NSCDC a jihar Neja, Suberu Aniviye, sakamakon mutuwar wasu matasa da ake zargin masu haƙar ma’adanai ne ta ɓarauniyar hanya.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayar da umarnin a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X inda kuma ya buƙaci a gudaar da cikakken bincike kan lamarin, da rahotanni ke cewa ya faru a yankin Wushishi/Lukoto da ke Mina, babban birnin jihar ta Neja.
A cewar sanarwar, an kama waɗanda ake zargi masu haƙar ma’adanai ne ba bisa ƙa’ida ba yayin samamen da aka kai a yankunan jihar a ranar Talata da kuma Laraba na wannan makon.
A cewar ministan, “muna tafiyar da gwamnati ce wadda babban abin da ta sa a gaba shi ne kare rayukan jama’a kuma muna aiki tuƙuru don tabbatar da hakan”.
Ya kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu sannan u ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda (BBC Hausa).































