Home Tsaro Dara taci gida: Yadda Yansanda 10 suka Fada Komar Yanbindiga a Kogi

Dara taci gida: Yadda Yansanda 10 suka Fada Komar Yanbindiga a Kogi

272
0
IGP
IGP

Al’amuran Tsaro kullum a Nageria kullum suna kara rikitar da duk mai bibiyar lamarin tsaro a Kasarnan.

Fadawar komar Yanbindiga da Yansanda goma da ga Jahar Nasarawa sukayi babban  abun dubawa bane. Koda yake wannan bashine na farko inda Yanbindiga sukeyin wuf da Yansanda, kai harma da Sojoji ba.

Wani lokacin har rayukan Yansandan da Sojoyin Yanbindigar suke dauka idan da karar kwana a wani hari na kwantar bauna.

Harin da aka kaiwa ayarin motocin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan hanyarsu ya zuwa Daura gabanin bikin sallah Babba wani babban al’amari ne da yake nunawa cewa akwai bukatar mahukunta musamman Jam’ian Tsaro su sake tunani  a wannan yaki da sukeyi da ta’addanci a kasarnan.

Rahotanni sunce Yansanda suna kan hanyarsu ta komawa Jahar Nasarawa ne, Yanbindigar sukayi awun gaba dasu a lokacin da motar da suke ciki mai lamba GWA 295 YR wadda direbansu Usman Abdullahi yake tukawa ta sami matsala a Obajana na Jahar Kogi.

Yansanda su 18 wadanda takwas daga cikinsu sun tsira sune suke bawa DPO Obajana labarin abun daya faru, cewa suna dawowa ne daga Jahar Osun bayan sun halarci zaben Gwamna da aka gudanar ranar Asabar data gabata.

DPO na Obajana ne ya sanar da cewa sunji karar bindugu  a wata hanya dakebi ta bayan garin ne suka kai dauki.

Amma kafin su karasa gurin tuni Yanbindigar sunyi awun gaba da goma daga cikin Yansandan kamar yadda wasu daga cikin Yansandan da sukayi gamo da katar suka sanar dasu.

DPO ya sanar da cewa rundunar Yansanda batayi kasa a gwiwa ba ta tura Jami’anta na musamman ko Allah zaisa a dace a kubutar da wadanda aka kama.

Jaridar Guardian t ace ta tuntubi rundunar Yansanda ta Jahar Nasarawa domim nema Karin bayani amma hakanta bai cimma ruwa ba harya zuwa lokacin da aka hada wannan labari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here