Home Uncategorized Tunawa Da Uwa Da Babu Irinta: Hajiya Hajara (Yelwa) Jibon Garama

Tunawa Da Uwa Da Babu Irinta: Hajiya Hajara (Yelwa) Jibon Garama

6
0
Hajia Yelwa 1

>  Ya Ga Madakin Dogaran Sarkin Kano –

(Muhammadu Sanusi, Muhammadu Inuwa, Ado Abdullahi Bayero)

>  Mata Ga Alhaji Dauda Sulaiman Ringim: 1945 – 2026 (91 Years)

Daga: Bashariyya Bashir Mudi

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Inna Lillahi wa Inna Ilaihi Raji’un.

(Asabar 12 ga watan Satumba, 2026 (29Maulud, 1447AH)

A yau mun tashi domin yin Ibadar Jana’izar wata rayuwa mai albarka. Rayuwar Hajiya Yalwa – Jibon Garama, ’yar wani Shugaba na Masarautar Kano, kuma matar, Alhaji Dauda Suleiman Ringim – Babban dan kasuwa kuma dan kwangilar Abinci daliban makarantar kwana a tsohuwar jihar, Kano; wato tun suna hade da jihar Jigawa ta yanzu.

WACE CE HAJIYA YALWA?

Ita ce matar da sunan ta ya tsaya da ma’anar Gaskiya, Aminci, Hakuri da Juriya wajen Ibada.

Shekara 91 da ta kasance a duniya sun cika da darussa masu tarin yawa.

A matsayin Uwa da Matar Aure: Ta zauna da mijinta – “Idealist” (mai hangen nesa), Alhaji Dauda Suleiman Ringim, tsawon sama da shekaru 60 cikin zaman lafiya.

Ba a taba jin wata hayaniya da ga kewaye gidan su ba ko kuma ja-in-ja da ga sauran abokan zaman tun da gidan na su gida ne na zaman Rinji wato gidan Gandu, gidan da ya ke dauke da gidaje kusan kashi hudu, kowanne da iyalin sa.

Wannan shi ne mafi girman darasi na biyayya da hakuri a zama na gida na hadaka.

A matsayin mai sana’ar Hannu (Confectionaries): Gireba, Dibulan, Alkaki kuma yar kasuwa me siyar da Fulawa, Madarar Gari da kuma kayan hadi kamar Yis’, Abokanan kasuwancin ta sun santa da suna na me GASKIYA da AMANA kudin ta gata ne Ga masu karamin karfi hannayen ta kamar yadda su ke ambatawa a bude su ke, talakawa masu karamin jari da marayu su na farin ciki da kasancewa da ita musamman lokacin farin ciki ko akasin haka.

A matsayin Uwa ta Ilimi : ‘Ya’yan ta kusan su sama da goma Maza da Mata ba wanda bai yi ilimin Addini da na zamani ba dukkan su hafizai ne Na izu sittin cif-cif haka akaratun zamani babu me matsayin kasa da Difloma, NCE, Degree da Digirgir (PhD) dukkan su, su na da manya manyan aiyuka a gwabnatin tarayya da kuma gwarazan ’yan kasuwa ta hanyar Zamani – “Internet”.

Daga cikin ’ya’yan ta da kuma jikoki akwai Administrators, Accountants, Lawyers, Injiniyoyi, manoma kuma makiyaya, da masu cinikin Ma’adanai musamman duwatsu na alfarma a jikoki tana da yan jaridu musamman mata.

MANYA MANYAN ‘YA’YANTA sun hada da:

  1.  Marigayi Mustapha
  2. Marigayi Aminu
  3. Hajiya Nafisa (Mama Dabuje)
  4. Hajiya Safiya
  5. Marigayiya Hajiya Talatu
  6. Kawu Nasiru
  7. Aunty Rukayya (Yadikko)
  8. Auwalu (Kawu Alti Babba)
  9. Jamilu (Kawu Alti Karami)
  10. Alhaji Hafizu
  11. Kawu Hadi
  12. Anty Rabi ‘Yar Auta

Dukkan su da ga Dauda Sulaiman Ringim kowacce ta na da ‘Ya’ya da jikoki masu albarka.

Wannan shi ne mafi girman gadon ta, GADON ILIMI.

A matsayin Jagoran ta Al’umma: Ta kasance mai Hikima, Aminci, Adalci, Jajurcewa, Hangen Nesa, Kawaici, Zamunci, Kyauta, Kunya, Girmama na gaba, da kuma Rukon Addini.

Rayuwarta ta kacokan ta kasance cikin hidima ga Addinin Musulunci.

GADON DA TA BARI:

Hajiya Yalwa ta bar mana darusa guda uku:

1. Za a iya yin arziki ba tare da da yaudara ba.

2. Za a iya yin aure na shekaru 60 zuwa 70 ba tare da Rikici ba.

3. Mafi girman jari a wannan duniya shi ne ’ya’ya masu ilimin addini da ilmin zamani.

A yau mun rasa gangar jikin Hajiya, amma ba mu rasa darussan ta ba domin suna nan tare da mu. Mu na rokon Allah SWT da Ya gafarta mata, Ya yi mata tukwici da lada mai tarin yawa,Ya sanya ta cikin Aljannah Firdausi.

Ya kuma bawa ’ya’yanta da jikokin ta masu albarka hakurin jure wannan rashin mai girma.

Ameen Summa Ameen.

Bincike / da rubutawa: BASHARIYYA BASHIR MUDI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here