Home Kotu da 'Yan sanda Majalisar Dattawa Ta Umarci Kwamitocinta Da Su Gaggauta Tattara Dokokin Kasarnan Da...

Majalisar Dattawa Ta Umarci Kwamitocinta Da Su Gaggauta Tattara Dokokin Kasarnan Da Aka Sakawa Hannu Na Kusan Shekaru 20

159
0
Sen. Kaka

Majalisar Dattawa ta umarci Kwamitocinta na Sharia da na Yancin Dan’adam da na Dokoki da ba tare da bata lokaci ba su fara shirye-shirye domin tattara Dokoki da aka yi a Kasarnan da ga shekara ta 2004 zuwa shekara ta 2023 a wani mataki na hade su guri guda.

Majalisar ta bayar da wannan umarni ne sakamakon wani Kuduri na gaggawa  da Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Borno ta Tsakiya , Sanata Kaka, Shehu Lawan ya gabatar a gaban Majalisar a ranar Talata.

Sanatan ya ce dalilin sa na gabatar da wannan Kuduri  shi ne ya lura cewa kimanin shekaru 19 kenan da aka tattara Dokokin Kasarnan wanda hakan ya haifar da rudani a Kasa in da ake amfani da Dokoki daban-daban ma su karo da juna.

Sanata Kaka ya kara da cewa ya lura ma cewa masu tallar littattafai akan titunan Najeriya su na dauke da Kundin na Shari’a irin daban-daban a Kasarnan; wanda hakan  koma baya ne a kasarnan.

Har ila yau, ya lura da cewa  Malaman Makarantu a Jami’a da Dalibai kai harma da Lauyoyi suma suna amfani da Kundin Dokokin na Kasarnan iri dabab-daban wanda hakan bai da ce ba.

Sanatan ya cigaba da cewa, tun wancan lokaci zuwa yanzu Majalisar Taraiya ta yi Dokoki masu tarun yawa wadanda Shugabannin Kasa daban-daban sun saka mu su hannu amma har ya zuwa yanzu ba a tattara wadannan Dokoki ba guri guda domin amfanar Yan Najeriya.

Sanata Kaka wanda ya karawa Yan Jaridu haske a ofishin sa ya ce Dokace ta sahalewa ofishin Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Taraiya da ya gabatar da wannan bukata ta tattara Dokokin na Kasa tare da hadin gwiwa da Majalisar Taraiya.

Sanatan ya kara da cewa idan aka har-hada wadannan Dokoki guri guda zai taimaka wajen gudanar da shari’a a Najeriya ba tare da kawo rudani ba.

In da ya ce a halin yanzu tabbas akwai rudani a yadda ake yanke hukunce hukunce a Kotunan Najeriya sakamakon bambance – bambance da ake samu a Kundun Shari’a.

Majalisar ta Dattawa umarci Kwamitocin nata das u hanzarta tuntubar Babban Lauyan Gwamnatin Taraiyar don fara tattara wadannan Dokoki guri guda ba tare da bata wani lokaci ba. Tare da sanar da ita halin da ake ciki, cikin sati biyu masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here