Home Diplomasiyya Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS Ta Sha Alwashin Yin Anfani Da Rundunar “Ko-ta-kwana”

Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS Ta Sha Alwashin Yin Anfani Da Rundunar “Ko-ta-kwana”

162
0
Ecowas Logo

Bayan taron ƙolinsu a kan juyin mulkin Nijar ranar Alhamis, ƙasashen Afirka ta Yamma sun amince da amfani da ƙarfin soji a Nijar “ba tare wani ɓata lokaci ba” don mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Mohamed kan mulki.

Yayin taron, shugabannin ƙungiyar Ecowas sun ce sun amince da tattaro wata rundunar “ko-ta-kwana” bayan sojojin da suka yi juyin mulki sun ƙi amincewa da tattaunawar diflomasiyya.

Ecowas na da tarihin tura sojoji don shiga tsakani a yankin Afirka ta Yamma, da matakin nasara iri daban-daban.

Wace ce Ecowas?

Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) wata gamayya ce ta ƙasashe guda 15 da aka kafa a 1975 don bunƙasa matsayin rayuwar al’ummar ƙasashe mambobinta su fiye da miliyan 350 ta hanyar tabbatar da daidaiton harkokin tattalin arziƙi da na shugabanci.

Mambobinta sun haɗar da Benin da Burkina Faso da Cabo Verde da Gambia da Ghana da Guinea da kuma Guinea Bissau.

Sauran su ne Ivory Coast da Liberia da Mali da Nijar da Najeriya da Saliyo da Senegal da kuma Togo.

Kafa rundunar Ecomog

Sau da yawa, ana kiran ƙungiyar Ecowas ta je ta shiga tsakani a yankin Afirka ta Yamma, ko dai ta taimaka wajen kawo ƙarshen rikice-rikicen basasa ko kuma ta sake mayar da shugabannin ƙasashen da aka hamɓarar daga mulki ko kuma ta tursasa wa shugabannin da suka ƙi amincewa su karɓi kaye a zaɓe.

A 1990, Ecowas ta ƙaddamar da wani aikin tabbatar da zaman lafiya da ba ta taɓa yin irinsa ba don kawo ƙarshen wani mummunan yaƙin basasa a Laberiya ta hanyar tura wata rundunar sojojin ƙasashen yankin, wadda ake kira da Dakarun Sa-ido kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta na Ƙungiyar Raya Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecomog)

An sake tura dakarun Ecomog a karo na biyu zuwa Laberiya a ƙarshen mugun rikicin da ya shafe tsawon shekara 14 wanda ya kawo ƙarshe a shekara ta 2003.

Ƙungiyar ta Afirka ta Yamma ta kare matakin shiga tsakanin bisa hujjar cewa rikicin ya haifar da illoli a ƙasashe maƙwabta.

Shiga tsakanin ya yi nasara ta wucin gadi wajen dakatar da zubar da jini da kashe-kashen ƙabilanci kuma tun daga sannan mutane da yawa ke kallon matakin a matsayin wani abin koyi na warware rikici a yanki irin na Afirka ta Yamma.

Sai dai dakarunta na da hannu a jerin take haƙƙoƙin ɗan’adam, a cewar Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan’adam ta Human Rights Watch.

Sauran muhimman shiga tsakanin Ecowas

Bayan shiga tsakanin da ta yi a Laberiya, dakarun Ecomog sai suka zamo sashen dakarun soji na Ecowas a hukumance.

Da gama aikinsu a Laberiya, dakarun Ecomog sun kuma gudanar da wani shiga tsakanin na tsawon shekara uku don kawo ƙarshen yaƙin basasa a Saliyo, inda suka mayar da Shugaba Ahmad Tejan Kabbah kan mulki a 1998.

Shekara ɗaya bayan nan, an tura dakarun Ecomog kimanin 600 don tabbatar da kiyaye zaman lafiya a Guinea-Bissau mai fama da yawan juyin mulki. Rundunar ta kuma tura wani rukunin sojoji har sau biyu zuwa ƙasar, na farko daga shekara ta 2012 zuwa 2020 bayan wani juyin mulki, sai kuma wani juyin mulkin da bai yi nasara ba a 2022.

A 2003, dakarun Afirka ta Yamma sun shiga Ivory Coast don bin diddigin aiki da wata yarjejeniyar zaman lafiya wadda daga bisani ta raba ƙasa gida biyu tsawon shekara takwas.

Bayan shekara goma, ƙungiyar ta tura sojoji zuwa Mali don su fatattaki mayaƙa masu alaƙa da Al-Qaeda da ke ƙara dannawa daga arewacin ƙasar.

A 2017, Ecowas ta tura dakarun soji kimanin 7,000 zuwa Gambia daga Senegal mai maƙwabtaka, don tilasta wa Shugaba Yahya Jammeh ya tafi neman mafaka kuma ya bar shugabanci ga Adama Barrow, wanda ya kayar da shi a wani zaɓe da aka yi.

Ɓaraka a cikin Ecowas

Idan Ecowas ta yanke shawarar tura dakaru zuwa Jamhuriyar Nijar, za ta gamu da gagarumin ƙalubale.

A duk shiga tsakanin da ta yi a baya, mambobin ƙungiyar Ecowas sukan samu rarrabuwar kai a goyon bayansu wajen amfani da ƙarfin soja. Akwai rarrabuwar kai tsakanin ƙasashe rainon Faransa ƙarƙashin jagorancin Ivory Coast da kuma ƙasashe rainon Ingila ƙarƙashin jagorancin Najeriya.

Duk wani matakin amfani da ƙarfin soja Nijar, zai iya fuskantar irin wannan tarnaƙi.

Akwai ma barazana daga ƙasashe maƙwabtan Nijar. Ecowas ta dakatar da sojoji masu mulki a Mali da Burkina Faso, su kuma sun ce duk wani matakin soja da za a ɗauka a kan Nijar, za su ɗauke shi a matsayin wani matsayin wata “shelar yaƙi” a kansu.

Nijar ta fuskar shimfiɗar ƙasa, ita ce ƙasa mafi girma a Afirka ta Yamma, don haka tura dakaru zai kasance wani gagarumin ƙalubale ga ƙungiyar Ecowas.

Tattara rundunar sojojin da za ta aika, na iya zama ƙalubale ga wasu mambobin ƙasashe kamar mafi girma a yankin wato Najeriya, suna fama da ƙalubalen tsaro a cikin gida kuma ba lallai ne su iya bayar da sojojinsu ba.

Akwai kuma batun kuɗi ga duk wani mamayen sojoji musammam ma a lokacin da gwamnatoci suke fama da tsadar rayuwa.

Ana ganin matakin diflomasiyya don kai wa ga zaman lafiya a matsayin hanya mafi dacewa ga dukkan ɓangarorin. Sai dai akwai masu cewa shi kansa zaman lafiyar ba abu ne mai sauƙi ba, kuma don kawo ƙarshen yawan juye-juyen mulki a yankin Sahel, sai Ecowas ta yi da gaske. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here