Home Siyasa Samar Da Tsaro A Zamfara: An Yabawa Kokarin Gwamna Lawan

Samar Da Tsaro A Zamfara: An Yabawa Kokarin Gwamna Lawan

144
0
Hon. Shinkafi

Dan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Karamar Hukumar Shinkafi da Zurmi a Majalisar Taraiya da ga Jihar Zamfara Hon. Bello Hassan Shinkafi, ya yabawa kokarin Gwamnan Jihar Dauda Lawan wajen ganin ya samar da tsaro mai inganci.

Dan Majalisar ya yi wannan yabo ne a wata hira da Yan jaridu a ofishin sa da ke Majalisar Wakilai a birnin Taraiya Abuja a ranar Alhamis da ta gabata.

Hon. Shinkafi ya ce matakai da Gwamnan ya ke dauka na ganin an sami ingantaccen tsaro a Jihar abun a yaba ne ganin yadda ya ke daukar matakai iri-iri domin a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar.

Ya ce gabatar da Kuduri a Majalisar Jihar na Samar Da wani Asusu da zai Tallafawa Tsaro da samar da wata Rundunar Tsaro ta Mutun 5,000 da Gwamnan ya yi abu ne mai kyau da zai samar da ingantaccen tsaro a Jihar.

Dan Majalisar ya ce ko da ya ke matsalar tsaro a Jihar gadar ta Gwamnan ya yi amma matakai da ya ke dauka ya nuna karara irin kishin al’umar sa da ya ke yi sabo da haka a matsayin sa na Dan Majalisar Taraiya zai ba shi duk irin gudunmawar da ya ke bukata wajen ganin an sami ingantaccen tsaro a Jihar.

Hon. Shinkafi ya ce hare-hare da ake samu a halin yanzu a Jihar ya na faruwa ne sakamakon matakai da Gwamnatin Jihar Katsina ta ke dauka shi ya sa Yan bindiga su ke kaura da ga Katsina zuwa Jihar ta Zamfara.

Dan Majalisar ya roki mutanen Jihar Zamfara da su cigaba da bawa Gwamnan hadin kai akan wadannan matakai da ya ke dauka wanda ya ce da ikon Allah barazanar tsaro za ta zama tarihi nan da dan lokaci kadan mai zuwa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here