Home Siyasa Atiku Ya Dakatar Da Yakin Neman Zabe A Ribas Don Gudun Aranagama...

Atiku Ya Dakatar Da Yakin Neman Zabe A Ribas Don Gudun Aranagama Da Wike-Kwamitin Yakin Zaben PDP

177
0

Kwana daya gabanin gudanar da gangamin yakin neman zabe na jam’iyyar PDP a jihar Ribas, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar ya janye kamfen din don abin da a ka zaiyana da gudun asarar rayuka.

 

Kwamitin yakin neman zaben PDP ta bakin jami’in kwamitin Yusuf Dingyadi ya baiyana cewa Atiku ya janye zuwa Ribas don kare lafiyar magoya baya daga sauya magana da gwamna Nyesom Wike ke yi, inda a yanzu ya ce ya amince a yi taro a filin wasa kana daga nan a juya zuwa filin jirgi ba zagawa cikin gari.

Dingyadi ya ce ba wai Atiku na tsoron wani abu na lafiyar sa ba don ya na da jami’an tsaro da za su rufa ma sa baya, amma ya duba sauran ‘yan jam’iyya ne da matakin ka iya jefa rayuwar su a hatsari.

Wike da ke jagorantar gwamnoni 5 da su ka yi wa helkwatar PDP tawaye ya lashe takobin kin mara baya ga Atiku don rashin jituwa mai tsanani tun bayan zaben fidda gwani.

Duk da Atiku ya yi nasarar shiga wasu daga jihohin gwamnonin da ba sa mara ma sa baya kamar Binuwai, Abia da Oyo, gangamin na Ribas zai zama mai wuya don yanda kusan kullum gwamna Wike ke cewa matukar shugaban PDP Iyorchia Ayu bai sauka ba don daidaita mukaman jam’iyya da na ‘yan kudu, to sam-sam ba za a sulhunta da shi ba. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here