Home Siyasa Majalisar Dattawa Ta Yiwa Yan Najeriya Albishir Na Ganin Canji A Yadda...

Majalisar Dattawa Ta Yiwa Yan Najeriya Albishir Na Ganin Canji A Yadda A Ke Aiwatar Da Kasafin Kudi A Kasarnan

78
0
Sen. Sani Musa

Majalissar Dattawa ta yi wa Yan Najeriya albishir cewa za a samu gagarumin canji da ga yadda aka sabo aiwatar da kasafin kudin kasarnan a shekara mai zuwa sakamakon tanade –tanade da su ka yi a cikin kasafin kudi na cike gurbi da su ka gabatar da rahoton sa a ranar Laraba.

Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Sani Musa ne ya sanar da haka ga Yan Jaridu jim kadan da ya gabatar da rahoton Kwamitin na sa a gaban Majalisar.

Sani Musa ya ce tanade – tanaden da suke cikin karamin Kasafin kudin su ne kashin bayan Babban Kasafin Kudin da ake sa rai Shugaban Kasa, Ahmad Bola Tinubu zai gabatar a sati mai zuwa in Allah ya kaimu.

Ya ce Kwamitin na sa ya yi duba na musamman akan irin makuden kudaden da su ke shiga cikin asusun Gwamnatin Taraiya da yadda farashin  Danyen Mai ya ke kara tashi a duniya.

Bayan haka Sanatan ya ce an samu kari mai yawa na yawan Danyen Mai da ake fitarwa da ga kasarnan wanda yanzu ana fitar da kimanin Gaggan Danyen Mai miliya daya da dubu dari bakwai idan aka kwatanta da yadda ake fitarwa a gwamnatin baya wanda baya kaiwa Gagga Miliyan daya wani lokacin.

Sanata Musa ya kara da cewa kasarnan ta samu Karin shigowar kudaden shiga wanda haka yana nufin cewa kasafin na shekara ta 2024 zai kai sama da naira Tiriliya 26.

Dadin dadawa, Sanata Sani Musa ya ce sun bayar da shawarar ga jami’an tsaro da su kara karfafa matakan tsaro a wurare da ake hakar Danyen Man Fetur. Ya ce hakan zai bayar da dama wajen samun Karin kudaden shiga ga kasarnan.

Sanatan ya kara bayani cewa sun yi duba akan hanyoyin samun kudi ta fannin hakan ma’adanai wadanda aka bawa wasu mutane dama da su rinka hakan ma’adanai don yin wasu abubuwa amma basa yi. Sai dai su shigo da abubuwan da ga waje wanda hakan ya sabawa alkawarin da aka yi da su.

Ya ce toshe irin wadannan hanyoyi tare da wasu hanyoyin ma zai taimaka kwarai wajen samawa kasarnan Karin samun kudin shiga. In da ya ce samun Karin samun kudin shigar na nufin samun Karin gudanar da aiyuka a kasarnan.

A na su bangaren ya ce, Majalisar za ta saka ido wajen ganin an aiwatar da kasafin kudin kamar yadda aka yi alkawari don ganin an samu cigaban da ake bukata a kasarnan a fannoni daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here