Home Mai da Iskar Gas Majalisar Wakilai Ta Sha Alwashin Samawa Yan Najeriya Saukin Farashin Man Fetur...

Majalisar Wakilai Ta Sha Alwashin Samawa Yan Najeriya Saukin Farashin Man Fetur A Kasarnan

126
0
Hon. Ikenga Ugochinyere Ikegwuonu

Majalisar Wakilai ta sha alwashin ganin ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ta samawa Yan Najeriya sauki dangane da farashin Man fetur a wani mataki na saukaka mu su tsananin rayuwa da su ke ciki.

Majalisar ta yi wannan alkawari ne a yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a kan harkar Man Fetur da ma su zrga-zirga da shi a kasarnan su ka yi da Kwamitinta mai kula da Harkar Mai, karkashin Jagorancin Shugaban ta Hon. Ikeaguwonu Ugochinyere da ya gudana a zauren Majalisar  a satin da ya gabata.

A ya yin da ya ke gudanar da jawabin maraba Hon. Ugochinyere ya fadakar da ma su ruwa da tsakin irin hakkin da ya ke karkashin Kwamitin na saka ido tare da bibiya wajen ganin dukkan Hukumomi da ke karkashin Kwamitin sun gudanar da aiyukan da ya rataya a kan su ba tare da wata matsala ba.

Ya ce wannan dalili ne ya sa Kwamitin bai yi kasa a gwiwa ba wajen kiran ma su ruwa da tsaki a kan hakar Man Fetur domin jin dalilin da ya sa za su shiga yajin aiki a satin day a gabata wanda hakan ka iya kara jefa Yan Najeriya cikin matsi na tattalin arziki da tu ni su ke ciki.

Dan Majalisar ya ce wannan ganawa ce ta sa a ka sami nasarar dakatar da barazanar yajin aikin da Kungiyar masu safarar Man Fetur ta NATO su ka yi; wanda hakan ba karamar nasara bace.

Kuma Kwamitin sa a shirye ya ke ya cigaba da daukar irin wadannan matakai wajen ganin an dakatar da duk wata matsala da ka iya jefa Yan Najeriya cikin hali na kaka na kayi.

Da ya ke yiwa Yan Jaridu Karin Haske a  kan batum Hon. Inuwa Garba mamba a kwamitin  ya ce wannan ganawa da  Kwamitin ya yi soma tabi ne wajen ganin sun ji  irin koke koken mambobin domin samo mafita a kan matsalolin da a ke ciki.

Hon. Inuwa Garba

Ya ce duk da cewa an mayar da Kamfanin Mai na Kasa wato NNPC            L karkashin Yan kasuwa a kwai bukatar Gwamanti ta saka ido wajen ganin cewa dokoki da ke gudanar da wannan Kamfani an yi shi yadda zai saukakawa Yan Najeriya domin Man mallakar Yan Najeriya ne.

Hon. Inuwa ya ce sun lura cewa dokoki da ke tafiyar da kamfanin an yi su ne ba yadda zai samawa talaka sauki ba sabo da haka su ka ga yiwuwar kawo gyare-gyare ta yadda Yan Najeriya za su sami sauki.

Ta hanyar samar da hanyoyi masu sauki wajen safarar Mai din ta hanyar amfani da bututun Mai da jiragen kasa domin a bun da ya sa farashin Mai ya ke tsada shi ne kudin dako da a ke biya da ga Kudu zuwa Arewacin kasarnan.

Dan Majalisar Wakilan ya yabawa Yan Najeriya hakuri na halin da suka sami kan su a ciki; in da ya ce Majalisar Wakilai karkashin Jagorancin Tajuddeen Abbas ta yi alkawarin za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta samawa Yan Najeriya sauki ta hanyar lalubo hanyoyi da za su saukaka yadda a ke zirga zirgar Mai a Kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here