Home Mai da Iskar Gas Majalisar Wakilai Ta Bukaci Sabbin Daburun Hakar Danyen Mai A Kasarnan

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Sabbin Daburun Hakar Danyen Mai A Kasarnan

267
0
Alhassan Ado Doguwa

Majalisar Wakilai ta nemi hadin kan Gwamnatin Taraiya tare da sauran ma su ruwa da tsaki akan yadda a ke hakar Danyen man Fetur wajen ganin Yan Najeriya sun ci gajiyar sa ta hanyar amfani da sabbin dabaru wajen hako da sarrafa shi.

Shugaban Kwamitin Danyen Mai na Majalisar Wakilai, Hon. Alasan Ado Doguwa ya baiyana wannan bukata bayan kammala  zaman kare Kasafin Kudi na Ma’aikatar Mai ta Kasa da ya gudana a yau Talata a zauren Majalisar.

Ya ce zaman na su na yau ya bada dama wajen tattauna matsaloli da bukatu da ake da su tare da lalubo mafita ta yadda za a ci gajiyar mai a Kasarnan. In da ya ce lokaci ya yi da za a fara tunanin yadda za a rinka tono mai wadatacce domin samar da ababen more rayuwa.

Ado Doguwa, ya ce Najeriya ta dogara da man fetur wajen samun kudin shiga sabo da haka akwai bukatar a yi amfani da kudaden man da aka  debo domin gina wasu harkoki da za su rinka kawowa kasarnan kudin shiga domin duniya ta fara tunanin daina amfani da mai a matsayin makamashi.

Dan Majalisar ya ce tun kafin tusa ta kwacewa Bodari ya kamata a fara tunanin me za a gina domin kaucewa barazanar da ta ke tunkaro Mai a duniya. “Kasashen Duniya tuni sun fara kirkoro wasu ababen hawa masu amfani da hasken Rana da  wutar lantarki sabo da haka, nan da wasu shekaru masu zuwa za a daina bukatar Mai a Duniya a matsayin makamashi. Sabo da haka ya kamata mu fara tunanin wasu hanyoyi na samu kudaden shiga.” in ji Doguwa.

Ya ce abun kunya ne yadda abubuwa suke tafiya a harkar Mai a Kasarnan in da mu na da Danyen Mai amma ba za mu iya sarrafa shi ba sai mun shigo da taceccen mai da ga wata Kasa da gazawa na kasa kula da Matatun Mai da mu ke da su a kasarnan da gazawa na samun Dalar Amurka sakamakon fitar da Danyen Mai da mu ke yi da sauran su.

Doguwa ya ce akwai bukatar a sake nazari ta hanyar yin dokoki da tsare-tsare da za su kawo karshen wadannan matsaloli da su ka addabi wannan Kasa ta yadda za a karfafi Yan Najeriya wajen samun arziki da kwanciyar hankali da zaman lafia me dorewa a Kasarnan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here