Home Siyasa Gwamnatin Taraiya Ba Da Gaske Ta Ke Ba Wajen Raya Ma’aikatar Mai...

Gwamnatin Taraiya Ba Da Gaske Ta Ke Ba Wajen Raya Ma’aikatar Mai – Inji Majalisar Taraiya

171
0
IMG 20231218 WA0094

Majalisar Taraiya ta ce a bisa la’akari da yadda Gwamnatin Taraiya ta gabatar da Kasafin Kudi na Ma’aikatar Man Fetur na Shekara ta 2024, ta lura cewa ba da gaske ta ke ba wajen ganin an inganta ma’aikatar domin samar da cigaban da ya kamata a kasar nan ba.

Majalisar ta baiyana wannan takaici na ta ne jimkadan bayan ta kammala sauraron Kananonin Ministocin Man Fetu da na albarkatun Kasa da su ka gurfana a gabanta ranar Litinin domin kare kasafin Kudin Ma’aikatun su a wani zama na hadaka da ya gudana a Majalisar.

Shugaban Kwamitin Mai na Majalisar Wakilai, Alasan Ado Doguwa wanda ya yiwa Yanjaridu karin haske kan yadda zaman ya kasance ya nuna takaicin Majalisar na ganin yadda aka gudanar da Kasafin kudi na Ma’aikatar. “Daga bayanan da aka gabatar mana, na Kasafin Kudi na Ma’aikatar Mai ya nu na cewa ba da gaske Gwamnati ta ke yi ba na ganin an inganta wannan Ma’aikata”.

Ya ce, ware kasa da N10Biliyan da aka gabatar a matsayin Kasafin Kudi na Ma’aikatar Mai ya nuna karara cewa Gwamnatin Taraiya ba da gaske ta ke ba na samar da cigaban da ake bukata a kasarnan. In da ya kara da cewa wannan Ma’aikata ita ta ke samar da kaso mai tsoka na tattalin arzikin kasarnan amma abun kunya a ce an ware mata yan wadannan kudade.

Hon. Doguwa ya kara da cewa Kasafin Kudin bai yi wani tanadi ba na ganin cewa matatun Mai da ke karsarnan kamar Matatun Mai na Warri da Fatakwal da Kaduna ba a yi mu su tanadi na ganin sun koma aiki ba musamman ganin yadda duniya ta ke fito da sabbin hanyoyin samar da makamashi.

Doguwa ya ce kamata ya yi a hanzarta wajen ganin an gaggauta tono Danyen Mai da ya ke kasarnan domin sayarwa ga kasashen Duniya tun kafin a daina amfani da shi. Ya ce alamu sun nu na cewa nan da shekaru kadan ma su zuwa ruwan Pampo zai zo ya fi Man Fetur daraja sabo da a na ta fito da sabbin hanyoyin makamashi kamar yin amfani da hasken Rana da Nukiliya da Iskar Gas da sauran su.

Bayan haka ya ce, kusan dukkannin kasashen Africa suma sun sami Man Fetur wanda hakan ya sa darajar sa ta fara raguwa a Duniya. Sabo da haka akwai bukatar a gaggauta hake Mai domin sayar da shi don a gina kasarnan da shi tun kafin a daina bukatar sa.

Har ila yau, Majalisar ta goyi bayan kalaman Tsohon Sarkin Kano ku ma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Muhammadu Sanusi II, wanda ya ce ina kudaden da ake samu sakamakon cire Tallafin Mai da a ka yi. In da Majalisar ta bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu da yayiwa Yan Najeriya bayani na wadannan kudade.

Majalisar ta ce ko da ya ke Dokarnan ta PIA da a ka yi, ta daukewa Ma’katar Mai da Hukumar NNPC wa su aiyuka da  s u ke yi sakamakon Cin gashin kai da Hukumar NNPC ta ke da shi. Sabo da haka Majalisar ta ce wa su aiyukan kamar raya yankuna na Al’umomin da su ke zaune a wurare da ake hakar Mai an ware mu su kaso 3 na abun da ake haka domin raya yankunan na su kuma su al’umar ne su ke da ka she kashe wadannan kudade don raya yankin na su.

Sabo da haka, Majalisar ta bukaci da a bu ga wannan Doka domin a rabawa sabbin mambobinta da ma Yan Najeriya domin su fahimci wannan Doka ta PIA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here