Home Tsaro BLOOMBERG: YADDA SHUGABA BUHARI YA ANSA TAMBAYOYI SHA BIYU

BLOOMBERG: YADDA SHUGABA BUHARI YA ANSA TAMBAYOYI SHA BIYU

238
0
PMB
PMB

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda bai cika bawa Yanjaridu dama ba suyi hira da sh mai tsawo; sai gashi kwanannan ya bawa kamfanin dillacin Labarai na Blooberg dama inda suka yi masa tambayoyi har guda goma sha biyu wadanda dukkaninsu ya bayar da amsarsu.  Ka biyomu domin ka ji wadanne irin tambayoyine da kuma amsoshinsu daya bayar:

T1:  – Alkawurna daka dauka lokacin yakin neman zabe sune zaka yaki Cinhanci da rashawa da inganta Tsaro da kuma Yaki da Chinhanci da Rashawa. Yaya zaka kwatanta irin nasarorin daka samu akan wadannan alkawura. Bayan haka mai yasa har yanzu matsalar Tsaro takici taki cinyewa da kuma hauhawar farashi daya addabi Yan Najeria?

A: – Zamu bar Najeria cikin inganci fiye da yadda muka karbeta. Cinhanci da Rashawa yana raguwa akasarnan domin kuwa muna hukunta masu laifi kuma ana dawo da kudaden da aka sata ka gayawa kowa haka. Yan ta’adda basu da wani iko a ko’ina a Najeria. An kashe shugabanninsu. Kuma mun gudanar da aiyukan raya kasa da yawa a dukkan sassan kasarnan domin kawo cigaba.

Batum Tsaro

A shekara ta 2015, wani sashe na Najeria yana karkashin inkon Yan Boko Haram wanda yakai girma kasar Belgium amma wannan yanzu ya zama tarihi. Shugabannin ISWAP sun sheka lahira saka makon rowan wuta da Jami’an Sojin Kasa sukai musu a watan Maris a sakamakon bayanan sirri da mukai hadin gwiwa da Kasar Amurka da Birtania.

Muna fatan irin wadannan kasashe zasu cigaba da bamu hadin kai ta hanyar aiyana Kungiyar IPOB a matsayin Kungiyar Yan Ta’adda. Shugabancin wadannan kungiyoyi yana samun mafaka ne a wadannan kasashe kuma ta nanne suke gudanar da aikace aikacensu na tunzura yan Najeria domin ayi tashin hankali. Da kuma kashe kudade masu yawa don ganin sunja hankalin yan Majalisar Kasashen domin su goyi bayansu. Munaso wadannan kasashe su taka musu birki.

Gwamnatinace kadai ta kawo karshen tashe tashen hankula tsakanin Manoma da Makiyaya ta hanyar samar da wani tsari na Noma da Kiwo na Zamani. Koda yake wasu Jahohi sun maida batum Siyasa amma duk da haka an sami gagaramin nasara.

Tattalin Arziki

Gwamnatinmu tana daukar matakai akan Tattallin Arziki domin munki bin ra’ayin wasu. Muna kokarin mu dogara da kanmu muka bunkasa yadda za’a rinka sarrafa abubuwan da muka Noma. Sai gashi Yaki da akeyi a Kasar Ukrain ya nuna karara cewa, matsala da ake fuskata a wasu kasashen Duniya akan makamashi da abinci; yasa suma sun chanza tunaninsu.

Mun shafe zango biyu da mukayi akan mulki muna aiki tukuru wajen gudanar da aiyuka da zasu kawo cigaba a kasarnan kamar gina tituna da Layin Dogo da inganta Zirga-zirga da sauran muhimman aiyuka wadanda ganin tasirunsu sai a hankali za’a gani.

Chinhanci da Rashawa

Mu fara da batum fallasa masu cChinhanci wanda Gwamnatina ta maida shi Doka a shekarar farko na Mulkina. An dawowa Najeria da miliyoyin kudade da aka kai wasu kasashe aka boye.

Tare da hadin gwiwa da wasu kungiyoyi na kasashen Duniya an dawowa da Najeria kudade miliyoyi iri daban-daban. Da farko daga Kasasashen Turai da Amurka da Siwazilan munyi amfani da irin wadannan kudade wajen Tallafin jinkai irin na Korona ga Talakawa marasa karfi. Wasu kuma kudaden munyi amfani dasu wajen manyan aiyuka da akayi watsi dasu shekara da shekaru kamar su tituna da tintin dogo da gadoji da kuma wutar Lantarki.

Bari in bada misali kamar da watan Janairu zuwa watan Disamba na shekara ta 2021 mun karbo kudi kimanin Naira Biliyon 152. Dalar Amurka kuma a wannan shekara miliyan 386 da GBP kuma 1.1 da kum Yuro 157,000 da kuma Riyal na Kasar Saudia Miliyan1.7 da kuma wasu kudaden da yawa a nau’I daban-daban.

Wadannan abokan hadin gwiwar tamu sunki su mayar da wadannan kudade ga Gwamnatocin da sukazo kafin mu saboda gudun kada a sake sace kudaden amma sabo da sun aminta damu suka dawo da wadannan kudade ga Gwamnati na sabo da yarda damu.

T 2: Tun shekara ta 2015 Hauhawar farashi yake ta cigaba a Najeria duk da irin yunkurinka na ganin an samar da kayan abinci anan cikin gida? Ta yaya Gwamnatinka take fuskanci wannan matsala? Shin Gwamnatinka ta damu da matsalar karancin abinci da ake fuskanta a wannan kasa tare da duba da Fari da yake addabar wasu sassan kasarnan?

A: Ya kamata ace munyi tunani cewa da badan wadannan matakai da muke daukaba na samar da abinci anan cikin gida da yaya farashin kayan abinci zai kasance a kasarnan duk da cewa bama iya samar da dukkan abincin da muke bukata.

Tsare –tsaren da muka fito dasu irin su Anko Barowa ya taimakawa Manoma mutuka wajen yin gogayya da kayan abinci marasa inganci da ake shigo dasu kasarnan. Hakan ya sa mun iya samar da Ton Miliyan Tara a shekara ta 2021 daga Ton Miliyan 5.4 da ake samarwa a shekara ta 2015. Koda a wannan shekara ma da ake fama da Fari, mun samar da Shinkafa fiye da abinda ake samarwa a 2015. Shigo da shinkafa ya kasance babushi kwata kwata, ina ganin muna samun nasara.

Duk da irin wadannan Tsarere na Duniya akan cinikaiya da kasashen Africa musamman Dokoki na kasashen Turai, lokaci yayi da Africa zata kulla sabuwar dangantaka da wadannan kasashe na Duniya. Duk wadannan zantuttukane da ake tayi akan wadata kasa da abinci koda yake anayiwa Africa wani kallo akan dogara da kai da Talauci da Fatara.

In badan bukatar kaiba irin ta kasashen Turai musamman Taraiyar Turai akan fadakar da mutanen Africa illar Kwarara zuwa wadannan kasashe – ya kamata su kara kaimi. Illoli da ake fuskanta ta Tarbiya da ta Tattalin arziki ba abu bane da za’ayi musu akansa ba. Idan Kasashen Turai basuyi wani abu akansa ba to, lallai za’a samu kwararar mutanen Africa zuwa Turai har wani lokacin a rasa rayuka masu yawa.

T 3: Batum wutar Lantarki matsala ce datakici taki chinyewa duk da irin kokarin da Gwamnatinka keyi. Wasu na kiraye kirayen a zamanantar da samar da wutar Lantarki. Kana ganin Gwamnatinka tayi abun daya dace kuma mai kake saran kayi anan gaba?

A :  Da farko muna bukatar Dokoki da zasu samar da kyakkyawan yanayi don inganta wutar Lantarki. Sannan ya samar da adalci wajen gudanar da harkar. Game da zamanantar da harkar Wutar Lantarki, aiyuka sunyi nisa, abun da ake bukata shine samar da kudade domin aiwatar dasu. Ka duba tsarin dana fito dashi wato PPI, tsari na gwamnati da gwamnati wanda hakan yasa Gwamnatin Germany da Kamfanin Siemens AG sun daga martabar wutar Lantarki da Dalar Amurka Biliyan Biyu a Najeria.

Idan aka gama gyare gyare a kundin tsarin Mulki kuma na saka masa hannu, hakan zai bawa jahohi dama su samar da wutar Lantarki ta kashin kansu. Har ila yau, zai bawa masu saka jari dama su saka jarinsu.

Munayin gyare gyare don ganin an samar da wutar Lantarki ta hanyar Sola. Kudade kimanin Dalar Amur miliyan 550 da aka samar zasu samar da kayan Wutar Sola 20,000 da kuma kananan injinan Solar a gurare 250 a Najeria.

T 4: Hukumar Lamini ta IMF da Bankin Duniya suna ta kiraye kiraye akan ka cire Tallafin Mai da kuma daidaita kudaden Musaya. Me yasa ba zaka amsa wannan kiraye kiraye nasu ba?

A : Dayawa daga cikin kasashen Duniya da sukeyin wannan kiraye kiraye suma basu cire Tallafin Mai ba a kasarsu. Don me mu zamu cire namu?

Abubuwan da suke rubuce a takarda danban da abubuwan da suke faruwa a zahiri – a faiyace suke. Gwamnatina tayi yunkurin cire Tallafi a bara amma sakamakon shawarwari na kwararru da kuma yadda abubuwa suke tafiya a halin yanzu, cire Tallafi zaiyi wuya a halin yanzu.

Inganta yadda za a samar da mai a cikin gida shine abun da muke bawa muhimmanci. Hadin gwiwa da Yan Kasuwa zai tallafa wajen samar da wadataccen Mai. Shirye shirye sunyi nisa wajen ganin Matatun Dangote da BUA da Waltersmith sun fara aiki.

Game da tashin kudaden misaya sakamakon kalu bale da duniya take fuskanta. Muna kokari muga mun inganta samar da kyakkywan yanayi don samar da abinci acikin gida da Mai. Abubuwa zasuyi sauki a hankali.

T 5: Basussuka da kasarnan ke ciyowa tun shekara ta 2015 yasa duk kudaden shiga da ake samu anayin amfani dasu wajen biyan bashi. Me hakan yake nufi da kasarnan anan gaba? Kana ganin Gwabnatinka tanayin abun daya dace wajen ganin biyan wannan bashi bai ta’azzarra kasarnan ba?

A : Karamin Tunani akan ciyo bashi zai sa mutum ya kaucewa hanya. Abun da akeyi shine samar da abubuwa da kasarnan ta rasa wadanda zasu tallafa mata wajen farfado da Tattalin Arzikin kasarnan. Kuma ana gudanar da aiyuka ne a dukkan sassan kasarnan domin magance matsaloli da ake fuskanta irin na rashin Tsaro.

Abubuwan da mukeyi, buri ne wanda ba’a tabayi ba tun bayan samun Yancin Kasarnan. Sama da tituna 800 na Gwamnatin Taraiya ake ginawa da sabuntawa. Titutunan Dogo mai nisan zango 650 aka samar wanda hakan yana tallafawa wajen saukaka farashin zirga zirga da kayan abinci.

Idan badan wadannan aiyuka ba gibin da za’a samu ba karami bane, wanda hakan zai karasa rayuwa tayi tsauri. Akwai bukata matuka na wadannan aiyuka domin kawo cigaba da kuma dauwa meman cigaba kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bukata.

T 6: Najeria na daga cikin kasashe dake da karancin karbar Haraji. Akwai abun da Gwamnatin zatayi na ganin ta kara samar da hanyoyin samar da kudaden shiga?

A : Duk da cewa Najeria na daga cikin kasashe mafiya yawan al’umma amma samar da kudaden shiga wani babban kalubale ne. Mun kara haraji a shekara ta 2020 amma hukumar Lamuni ta Majalisar Dinkin Duniya tanaso mu sake karawa. Wannan wani abu ne mai wuya a halin da ake ciki. Kashi 80 na ma’aikatan Najeria daga kananan sana’oi suke rayuwa. Ta yaya zaka kara haraji akan matsin da suke ciki.

Munayin kokari dai muga an sami mafita. Mun kara samar da Katin Dan Kasa daga Miliyan 7 a shekara ta 2015 zuwa miliya 90 zuwa 100 a halin yanzu tare da samar da Lambobin Haraji da suaransu.

A shekara ta 2016 mun samar da Tsari na Inganta Yanayin kasuwanci wanda zai bawa Yan Najeria dama su gina kasuwanci su tare da tallafin Katin Shedar Dan Kasa. Munayin kokari tare da Kungiyar ECOWAS wajen ganin an saukaka kasuwanci tare da samar da kudaden bai daya a yankin.

T 7: A matsayinka na Ministan Mai kuma Shugaban Kasa. Me yasa Najeria ta kasa fidda adadin Man da Kungiyar Kasashen Masu Arzinkin Mai na OPEC suka bata dama duk da Karin farashi da ake samu a Duniya? Me kakeyi akan wannan Lamari?

A : Shekaru hudu da suka gabata mun kaddamar da shimfida bututun Mai daga Najeria zuwa Turai. Kamfanin NNPC tare da hadin gwiwa da Kungiyar ECOWAS ya saka hannu akan Yarjejeniya a ranar biyu ga watannan na Yuni don tabbatar da hakan.

Ranar Daya ga watan Yuli, Kamfanin NNPC zai zama Kamfani mai zaman kansa wanda hakan zai bada dama wajen bibiyar aiyukan da yake gudanarwa. Hakan zai bada dama mutane su saka jari da kuma saka ido akan yadda ake tafiyar da kamfanin. Wannan abun alfari ne a Gwamnatina aka samu wannan nasara. Gwamnatocin baya sun gaza a wannan fanni.

Aikin Yan Ta’adda ya shafi kokarinmu na samar da Mai. Kungiyoyi irin su IPOB, shi yasa muke sa a baiyanasu a matsayin Kungiyar Yan Ta’adda domin suna fasa bututun Mai wanda hakan yayi sanadiyar koma baya wajen samar da Mai da ake bukata domin fiddashi waje.

Munkashe kudade masu yawa a harkar Tsaro, harda Dalar Amurka Biliyan Daya da muku kulla yarjejeniya da Kasar Amurka domin Mallakar jirgnin yaki A -29 Super Tukano. Hakan yasa ana samun gagaramin nasara wajen yaki da ta’addanci wanda yasa OPEC ta kara mana yawan Mai da zamu fitar a wata mai zuwa.

T 8: Me Najeria takeyi wajen ganin taci gajiyar karancin Iskar Gas  da yake faruwa a Turai. Ya zuwa wane lokaci Nageria zata cike gibin bukatar Iskar a Turai?

A : Muna bukatar kulla abota ta dindindin ne ba wai kawai muyi amfani da wani yanayi ba don samun biyan bukata na kankanin lokaci. Samar da jari shine babbar matsalar samar da Iskar Gas da akayiwa lakabi da Green. Anan cikin gidama itace matsalar. Wadannan matsaloli basu taimaki Kasashen suba na Turai haka zalika muma bai taimakemu ba. Wannan wata makarkashiyace wacce dole a kawo karshenta.

Domin chanza wannan al’amari dole sai Turai da Taraiyar Turai sun saka jari don samar da Iskar Gas daga turun Iskar da muke da ita zuwa Turai daga Najeria, mai nisan kilomita 4000 wanda zaibi ta Marocco zuwa Turai.

T 9: Kana da sha’awa na ganin cewa Babban Bankin Kasarnan CBN ya tsaya da kafafunsa; lura da yadda Shugaban Bankin yake kokarin ganin ya tsaya Takarar Shugaban kasa? Ta yaya zaka warware wannan matsala?

A : Gwamnan Babban Banki Shugaban Kasa ne yake nadashi bayan ya sami sahalewa daga majalisar Taraiya. Kwamitin Gudanarwa na CBN yake da ikon duba hukunce hukunce don tabbatar da ganin an bi Dokoki na gudanarwar na Bankin ko a’a. Ko Gwamnan Bankin yabi Dokokin ko kuma ya karyasu wannan wani abune daban.

Akwai kuma wani bahasi akan abun da Gwamnan yayi na shiga wani bangare daba na Banki ba, ance hakan Siyasa ce amma kuma wani lokaci ya karyata hakan. A maimakon hakan, Gwamnan yanayin abubuwa da Dokoki suka tanada don inganta rayuwar marasa karfi. Ya kamata abar Najeria ta zabi tsari daya dace da ita don inganta tattalin arzikin kasarnan sobo da Yan Najeria.

T 10: Shin kana da burin ka nuna dantakarar da kake goyawa baya. Idan kana dashi kuma waye?

A: Eeh! Zan nuna dan Takarar da APC ta zaba da zaiyi Takarar Shugaban Kasa.

T 11: An jiyoka kana bada shawara akan taro da za’ayi na kasashe renon Ingila a Rwanda wata mai zuwa; taron zai bada muhammanci akan batum Tsaro da kare Kai. Menene a zuciyarka a game da wannan taro da za’ayi ?

A : Africa itace mafi girma daga cikin kasashen rainon Ingila. Sabo da haka babu wani dalili da zaisa ta kasance Kasa da take da alaka da wannan yanki ba game da cinikayyar makamai ba. Saidai idan ba’a samu anan ba, sai aje wani gurin.

A maimakon hakan, akwai bukatar ayi amfani da arzikin da Allah ya horewa kasashen. Bayan haka akwai bukatar amfana ta fannin hadin gwiwa da kuma bayanan sirri.

Nayi amanna cewa, Kungiyar za’a iyayi amfani da ita wajen neman kuri’a akan batutuwa da suka shafi kasashen kungiyar a yayin tarurruka na Duniya da kuma jin ra’ayin yan kungiyar akan batutuwa da suka shafesu. Me zaisa ba zamu kasance tare dasu ba.

Har ila yau za’a kuma iyayin amfani da kungiyawar wajen magance wasu tarnaki da ka iya kawo cikas ga Yan Kungiyar. Misali Yunkurin da Ingala takeyi na ficewa daga EU, Yan Kungiyar zasu iya maramata baya musamman idan akwai yiwuwar bunkasa tattalin arzikin. Turaice kasa ta farko data kulla alaka ta kasuwanci da Kungiyar AfCFTA.

Africa tana da mamba guda 19 wanda hakan itace lamba mafi girma a Tattalin Arziki a cikin Kungiyar. UK-AfCFTA shine sashi mafi girma da ya kulla alaka da Kungiyar Renon Ingila. Kasashen Renon Ingila kamar su Australia da Canada zasu saka hannu akan yarjejeniya da kowa zai amince da ita.

T 12: Shin ka damu da yadda ake jefe wadanda suke kalamai na batanci a Arewacin Nigeria. Ya Kake kallon wannan al’ada a zamantakewa Nageria anan gaba?

A : Ba wani mutum da yake da iko na ya dauki Doka a hannunsa. Addinin Musulunci dana Kirasta sunfi kusa da juna fiye da suaran addinai kamar yadda muka gani a littattafansu guda biyu. Yan Najeria suna da tarihi na mutumta juna tun tale-tale, toh ya kamata mucigaba  da mutumta juna kuma ya kamata mu fahimci juna.

Abun daya faru baiyiwa kowa dadi ba kuma ya kamata mu mutumta bambamce-bambamce dake tsakanin mu.

# KARSHE#

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here