Home Kotu da 'Yan sanda Mai Shari’a Bulkachuwa ta musanta maganar mijinta

Mai Shari’a Bulkachuwa ta musanta maganar mijinta

196
0
Zainab Bulkachuwa

Tsohuwar Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa ta musanta kalaman da mai gidanta ya yi na cewa ya yi amfani da damarsa, wajen nema wa abokan siyasarsa Sanatoci alfarma lokacin da take aiki a matsayin alkaliya.

Cikin wata gajeruwar sanarwa, Mai Shari’a Zainab ta ce cikin tsawon lokacin da ta kwashe tana aiki ba ta taba yi wa wani mutum amfarma ba a duk tsawon shekaru gommai da ta kwashe tana aiki a zaman mai shari’a.

Tsohuwar shugabar kotun daukaka karar, wacce ta shafe shekaru arba’in tana aikin shari’a, ta ce masu shari’a a karkashin jagorancinta za su iya bayar da shaida a kan cewa ba ta taba tsoma baki ga ‘yancin kansu ba.

“ An jawo hankalina kan bidiyon abin da mijina, Sanata Adamu M. Bulkachuwa ya fada. Ina so in bayyana a fili cewa ban taba saba rantsuwar da na yi don nuna fifiko ga wani bangare da ya gurfana a gabana ba cikin shekaru 40 da na kwashe ina hidimta wa kasata ba’’.

Yadda lamarin ya samo asali

Tun farko dai wani bidiyo da aka naɗa da ya karaɗe shafukan sada zumunta ne ya nuna Sanata Bulkacuwa yana jawabin bankwana a cikin zauren majalisar dattijai yana mai cewa:

“A cikin zauren nan, ina iya ganin fuskokin da suka zo, suka nemi taimakona lokacin da matata take shugabar kotun daukaka kara ta kasa”.

Sai dai yana cikin bayani ne sai tsohon shugaban majalisar dattijai Ahmed Lawal ya katse masa hanzari tare da yi ma sa hannunka mai sanda.

“Irin wadannan kalamai masu harshen damo za su iya nuna an samu alfarma ko wani abu makamancin haka”, in ji Sanata Lawal

A yanzu haka kungiyar lauyoyi ta Najeriya NBA ta aike da wasika a hukumance zuwa ga babban sufeton ‘yan sandan kasar, da kuma hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC da EFCC .

Kungiyar ta nemi bangarorin uku da su gudanar da bincike a kan Sanatan.

Wasu masu fafutuka sun nemi a hada har da matarsa da ya ambata a cikin binciken.

Ce-ce-ku-ce

Wannan ne dai karo na biyu da Mai Shari’a Bulkachuwa ta tsinci kanta a irin wannan yanayi na musanta zargin da ake yi mata na aikata ba dai-dai ba, domin ko a lokacin da take shugabantar kotun daukaka kara, mukamin da ta rike tsakanin watan Afirilun 2014 zuwa Maris 2020 ta tsinci kanta a zargin cin hanci.

A kwanakinta na karshe kafin ta yi ritaya daga aiki, cikin watan Fabarairun 2020, ta yi wata ganawa da manema labarai a Legas, inda ta musanta zargin cewa ta karbi cin hancin Naira biliyan 6.

“Akwai lokacin da zarge-zarge ke ta yawo cewa an ba ni Naira biliyan 6, sai na yi dariya, da a ce an ba ni Naira biliyan 6 kuna tsammanin zan ci gaba da kasancewa a nan ne?” In ji ta.

A shekaarar 2019 ma babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta nuna rashin amincewa da Bulkachuwa a matsayin shugabar kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, kasancewar mijinta dan jam’iyya mai ci ne ta APC. (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here