Home Siyasa Majalisar Wakilai Ta Yi Alkawarin Ganin Shugaban Kasa Ya Saka Hannu A...

Majalisar Wakilai Ta Yi Alkawarin Ganin Shugaban Kasa Ya Saka Hannu A Kan Dokar Mafarauta

1763
0
Hon. Balele

Majalisar Wakilai ta ce zata yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin Fadar Shugaban kasa ta tabbatar da Dokar nan ta Mafarauta wadda aka fi sani da “Hunters Bill” a wani mataki na ganin an samar da tsaro da zaman lafia mai dorewa a kasarnan.

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan Hukumomin Dutsin-Ma/Kurfi Honorabul Aminu Balele ne ya sanar da haka lokacin da shugabancin Kungiyar ya kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja ranar Laraba.

Honorabul Balele ya ce, dalilin da ya sa Majalisar Wakilai ta amince ta sake gabatar da Kudurin duk da yake Majalisa ta 9 ta amince da Kudurin, harma ta tura shi ga Fadar Shugaban Kasa domin a sakawa Dokar hannu amma hakan bai samu ba a gwamnatin da ta gabata.

Ya ce muhimmanci kudurin ne ya sa Majalisa Wakilai ta 10 ta sake dawo da kudurin domin ganin ya zama Doka ba tare da bata lokaci ba.

Balele ya kara da cewa, Mafarauta suna da masaniya akan dukkanin dajujjukan dake kasarnan kuma bata gari sunayin amfani da dajujjuka ne wajen aikata barna irin ta karbar kudin fansa kuma anan ne suke boyewa idan sun aikata wani laifi.

Ya ce idan anyi wannan Doka zata bawa Mafarauta dama suyi aiki kafada da kafada da sauran jami’an tsaro wajen ganin an kama masu laifi kuma an hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Honorabul Balele ya kara da cewa ba wani cigaba ta zai tabbata idan babu zaman lafiya. Kamar Noma ya ce b azai tabbata ba idan ana kashe Manoma ko kuma ana yin garkuwa da su domin neman kudin fansa.

Hon. Balele 2

Haka zalika sauran sana’o’i ma ba za su gudana ba indan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali. “Shi ya sa Yan Majalisar Wakilai su 359 suka amince da wannan Kuduri da na gabatar da shi a zauren Majalisa kuma tuni an Mika Kudurin ga Kwamiti domin ya bibiye shi” inji Honorabul Balele.

A wani bangaren kuma Honorabul Aminu Balele ya ce da ga zuwan sa Majalisa a kasa da wata guda ya gabatar da Kuduri guda 3 da kuma Doka ta gaggawa guda daya badon komai ba sai don ya  sauke alkawarin da ya daukawa mutanen sa na samar da Kudure – kudure da za su inganta rayuwar su.

Inda ya ce batum tsaro shine na farko sai kuma batum Noma da kuma Ilimi amma dukkannin su ba zasu samu ba sai harkar tsaro ta inganta shi ya sa ya gabatar da Kudurin Mafarauta domin sune kashin bayan samar da tsaro mai dorewa a kasarnan.

Tunda farko a nasa jawabin Shugaban Kungiyar Hunter  Amb Osatimehin Joshua ya yabawa Majalisar Wakilai da ta sake karkade Kudurin domin sake gabatar da dashi a Majalisar da kuma yin gyara don ganin an sake gabatar da shi ga Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka masa hannu ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban Hunters ya ce dalilin su na kaiwa Honorabul Balele ziyara shine sabo da shine ya gabatar da Kudurin a gaban Majalisar. Kuma hakan ya nuna karara irin kishi da yake da shi wajen ganin an samar da tsaro da zaman lafiya a kasar nan.

Kungiyar ta godewa Honorabul Balele tare da nuna jin dadinta wajen ganin Majalisar Wakilai tana goyon bayan irin gudunmawar da su ke bayarwa ga al’ummar Najeriya.

Shugaban ya kara da cewa sanin kowa ne Mafarauta su na sadaukar da rayukan su da dokiyoyin su wajen ganin kasarnan ta zauna lafiya ta hanyar bawa jami’an tsaro bayanai da goyon baya a yunkurin da gwamnati take yi na samar da tsaro a kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here