Home Siyasa INEC TA TABBATARWA YAN NAJERIA CIGABA DA YIN RIJISTA

INEC TA TABBATARWA YAN NAJERIA CIGABA DA YIN RIJISTA

224
0
INEC CHAIRMAN
INEC CHAIRMAN

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya jaddada yunkurin Hukumarsa na ganin an  sami wadatattun masu kada kuria  a zaben da za’a gudanar a shekara ta 2023.

Farfesa Yakubu ya tabbatarwa ‘yan Najeria cewa baza a rufe rajistar zaɓeba harsai Hukumar ta gamsu da cewa jama’a sun yi amfani da dammar ƙarin wa’adin da za ta yi, sun yi rajista sosai.

Jaridar Premium Times  tarawaito Yakubu yana cewa mutane su kwantar da hankulansu, INEC baza ta rufe yin rajistar zaɓeba a ranar 30 ga Yuni ba, 2022.

Shugaban na INEC yayiwa Yan Najeria albishirin ne yayin da yakewa dandazon matasa jawabi a Tsohon Dandalin Fareti a birnin Taraiya Abuja.

HumarZabe Mai ZamanKanta ta Kasa, INEC reshen Jahar Kano tace a cigaba da yin register da Hukumar keyi na Masu Zabe; Samari na daga Kangaba wajen yin rejista wadnda da suka kai yawan mutum  Miliyan 6,081,456 daga cikin mutum Miliyan 10,487,972 da sukayi rijista a zango na hudu na watan Yuni na shekara ta 2022.

Hukumar INEC a nan Jahar Kano  wacce take sanarwa da irin cigaban da ake  samu duk sati ta aikewa da Jaridar viewfinderng.com; wanda tace Matane kibiyewa Samari baya da mutum miliyan 4,339,006;  sai kuma Maza da suke da  mutum miliyan 4,292,690.

Ana gudanar da yin rijitan ne ta Yanar Gizo-gizo da kuma zuwa da kai; wadanda sukaje da kansu suna da adadi na mutum miliyan 5,381,247; wadanda kuma sukayi ta Yanar Gizo-gizo sun kai mutum miliyan 3,250,449. Yayin da masu bukata ta musamman da sukayi rijista sunkai mutum dubu 67,171.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here