Home Siyasa Bayanan Atiku Abubakar soki-burutsu ne — Tinubu

Bayanan Atiku Abubakar soki-burutsu ne — Tinubu

181
0
Tinubu dariya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da bayanan da abokin takararsa na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar, ya yi, cewa ya tattara isasshiyar shaidar da za ta tabbatar wa kotu, cewa shugaban kasar ya gabatar da takardar shaidar karatun digiri ta bogi ga hukumar zabe.

Shugaban Najeriyar, ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe, dangane da gabatar da wata hujja, idan ma akwai ta a shari’ar zaben shugaban kasa.

Cikin wata hira da BBC, mai magana da yawun shugaban kasar Abdul’Aziz Abdul’Aziz, ya ce abin da shi tsohon mataimakin shugaban kasa ya fada su a wajensu abu ne na su tausaya masa.

Ya ce, “ Wadannan bayanai na Atiku abu ne na a yi masa jaje saboda ya nuna cewa a cikin rudani yake bai ma san abubuwan da ke faruwa ba.”

Abdul’aziz Abdul’aziz, ya ce ita jami’ar da ake magana a kanta ta jihar Chicago da ke kasar Amurka a dukkannin takardu da bayanai da suka ba wa kotu babu inda suka ce akwai takardar bogi ko kuma shi Tinubu bai yi karatu a wajensu ba.

Ya ce, “ Bisa la’akari da wannan hujjar shi dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya yi maganganu ne wadanda yawancinsu na soki-burutsu ne da kuma kokarin yi wa mutane bayanan da za su dugunzuma su ko ma su kawo rashin fahimta.”

Mai magana da yawun Shugaba Tinubun, ya ce babu wata magana ta a zo a gani, borin kunya ne irin na wanda ya sha kaye.

“ Ko da mutumin da bai yi karatun lauya ba ya san cewa kotunan da suke na daukaka kara ba kotuna ba ne na yin shari’a, kotuna ne na duba hukuncin da kotun kasa ta yi domin idan akwai kuskure sai a gyara ko a canja wannan hukunci ko ma a tabbatar da shi.” In ji shi.

Abdul’aziz, ya ce, idan Atiku Abubakar na tunanin ya samo wata hujjar da yake gani zai iya gabatarwa ai bakin alkalami ya riga ya bushe.

Ya ce , “ Ba mu da wata fargaba saboda duk abin da ya kamata a yi an yi don abin da ake bukata wannan makaranta da ake ta magana a kanta ta riga ta bayar.”

“ Sannan mun san cewa duk abin da yake yi ba shi da tasiri kuma ba shi da wani gurbi na shari’a,” in ji shi.

Mai Magana da yawun shugaban na Najeriya, ya ce ya kamata yanzu Atiku Abubakar ya gane cewa an rufe babin siyasa kamata ya yi a fuskanci babin gina kasa kawai kamar yadda shi Shugaba Tinubu ya sha fada. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here