Home Diplomasiyya Afirka ta Kudu ta nemi Kotun Duniya ta ba da sammacin kama...

Afirka ta Kudu ta nemi Kotun Duniya ta ba da sammacin kama Netanyahu

139
0
Netanyahu

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi kira ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta ba da sammacin kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a tsakiyar watan Disamba.

Minista a fadar shugaban kasa Khumbudzo Ntshavheni ta ce matukar kotun manyan laifuka ta ICC ba ta yi hakan ba, matakin zai ba da alamun wata “gazawa gaba daya” cikin al’amuran tafiyar da mulkin duniya.

“Bai kamata duniya kawai ta tsaya kerere tana kallo ba,” in ji ta.

Isra’ila ta ce tana kare kanta ne daga harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai mata, wanda ya yi sanadin kashe akalla mutum 1,200 da kuma sace fiye da mutum 200, don yin garkuwa da su.

Ta ce tana kokarin takaita mutuwa da raunata fararen hula sai dai Misis Khumbudzo Ntshavheni ta ce gwamnatin Isra’ila na kokarin “kakkabe Falasdinawa daga akasarin yankin Gaza don ta mamaye”.

Afirka ta Kudu da Bangladesh da Bolivia da Comoros da Djibouti, duk sun gabatar da korafi a gaban kotun hukunta manyan laifuka don ta gudanar da bincike a kan ko an aikata laifukan yaki da laifukan keta hakkin bil’adama a Gaza. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here