Home Siyasa ‘APC na amfani da bangaren shari’a domin murkushe jam’iyyun hamayya’ – Atiku

‘APC na amfani da bangaren shari’a domin murkushe jam’iyyun hamayya’ – Atiku

153
0
Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya wuce , Atiku Abubakar ya yi zargin cewa jam`iyyar APC mai mulki na amfani da bangaren shari`a da nufin murkushe jam’iyyun hamayya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi misali da hukuncin da kotunan daukaka kara suka a yanke a wasu jihohi, ciki har da Zamfara da Filato da Kano da Nasarawa, yana cewa gwamnati na rabewa ne da shari`a wajen kwace jihohin da ke karkashin ikon jam’iyyun adawa.

Sai dai jam’iyyar APC ta musanta zargin

Atiku Abubakar ya ce sun lura da take-taken jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, kuma sun fahinci cewa da sannu tana nema ta murkushe hamayya baki daya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa APC na amfani da karfi wajen yin magudi ko rabewa da bangaren shari’a wajen soke nasarar da `yan hamayya suka samu a wasu jihohi, ciki har da jihohin Kano da Zamfara da Filato da kuma Nasarawa.

Mataimaki na musaman ga dan takaran shugaban kasar, Mallam Abdurrashid Shehu ya shaida wa BBC cewa Jam’iyyar APC mai mulki na kokarin karya dimokradiyya kasar ne

” Wannan bangare na sharia, bangare ne da yake cin gashi kansa amma yadda mu ke zargin sun yi kutse wajan shiga wannan bangare tare da yin kokari da yukurin karbar wasu jihohi, idan ka duba jihohi ne da suka fito daga jam’iyyun hammaya”, in ji shi.

‘Atiku na neman ya zama mai magana biyu’

Sai dai jam’iyyar APC ta yi fatali da zargin, tana cewa tsohon mataimakin shugaban Najeriyar na nema ya zama mai magana biyu. Mallam Bala Ibrahim shi ne Daraktan yada labarai na jam’iyyar:

“ A baya Atiku Abubakar ya jinjina wa bangaren sharia saboda bangaren shariar nan ya rika taimakonsa yakin da ya rika yi da tsohon shugaban kasa, cif Olusegun Obasanjo”

“Abin da kullum ya ke cewa shi ne bangaren shari’a shi ke ceton dimokradiyya, toh yau kuma saboda abubuwa sun sauya bangaren shari’a kuma ya zama wurin zargi da duk wasu abubuwa na batanci, wannan ba dai dai bane”. In ji shi

Wannan batun shari’ar dai shi ne ya sha gaban manyan jam`iyyun siyasa, da masu mulki da `yan hamayya, a jihohin da ake wannan ka-ce-na-ce a kan su, lamarin da ya sa da dama suka koma ga Allah.

Alal misali jihar Nasarawa na cikin wuraren da suka dukufa suna adu`a.

Hon Adamu Musa Alkali shi ne mai taimaka wa gwamnan jihar a kan harkokin siyasa:

” Wannan zabe yancin mutane ne suka dauka, suka bamu saboda yada da suke da shi a kan gwamnati, to mu ka ga abinda ya dace a wannan lokaci illa mu da tsaya da adu’a. Allah ya ba gwamna nasara a kotun daukaka kara”, in ji shi

Shi ma Mista Mike Omeri jigo ne a jam`iyyar PDP a jihar Nasarawa, ya ce sun saba da sanya adu`a cikin lamarinsu:

“ Tun farko a tafiyar David Ombugadu an fara da adu’oi ne da sauransu, musulmi da kirista suna nan suna adua’a, ana kokari ne domin a tabbatar cewa duk wanda ya yi nasara, nufin Allah ne” in ji shi .

`Yan magana dai kan ce shari`a sabanin hankal a don haka kan `yan Najeriya da dama ya daure, kuma hankalinsu ya koma kan bangaren shari`a wajen ganin yadda za ta kaya a kotuna daban-daban da ake kalubalantar nasarar da wasu gwamnonin suka samu a zaben da ya wuce. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here