Home Siyasa Zaben Neja: APC Ta Yi Nasara A Kananan Hukumomi 22 Daga Cikin...

Zaben Neja: APC Ta Yi Nasara A Kananan Hukumomi 22 Daga Cikin 25

283
0

Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 22 cikin 25 na kujerun shugabannin kananan hukumomin da hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Neja, NSIEC ta shirya a ranar Alhamis.

Daraktan Ayyuka na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja, Kwamared Ibrahim Aliyu Tunganwawa, ne ya sanar da sakamakon zaben a Minna.

Ya bayyana cewa ana dakon sakamakon sauran kananan hukumomin uku, inda ya ce jam’iyyun siyasa 13 ne suka shiga zaben.

A cewarsa, “Saboda wasu matsalolin da aka fuskanta a lokacin gudanar da zaben kansilolin kananan hukumomi, NSIEC za ta sake gudanar da zabukan a unguwanni biyu na kananan hukumomin Rafi da Kontagora.

“Yankunan biyu sune na Kusherki da Tungan Kawo da aka shirya gudanarwa a wannan Lahadi”.

Daraktan ayyuka na NSIEC, ya bayyana zaben kansilolin kananan hukumomin da aka gudanar cikin lumana da kwanciyar hankali tare da haifar da kananan matsaloli a kananan hukumomi uku da ake dakon sakamakonsu wanda suka hada da Katcha Agwara da Borgu. (Leadership Hausa).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here