Home Diplomasiyya Dalilin Da Ya Sa Ba Za Mu Iya Kwaso ‘Yan Najeriya Daga...

Dalilin Da Ya Sa Ba Za Mu Iya Kwaso ‘Yan Najeriya Daga Sudan Ba- Abike Dabiri

230
0

Hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare ta ce babu wata hanya da za a iya kwashe ‘yan Najeriya da rikicin Sudan ya rutsa da su, tana mai cewa yunkurin yin hakan na da matukar hadari.

Wata sanarwa da shugabar hukumar Abike Dabiri Erewa, ta fitar a ranar Juma’a a shafin Twitter, ta ce akwai yiwuwar duk jirgin da ya sauka a kasar a kona shi.

A cewar Dabiri, a jiya Juma’a, an kona duka jiragen da ke filin tashin jirage na Khartoum kuma an saka dokar hana zirga-zirga.

“Babu wani jirgin da zai iya aiki.” In ji Dabiri.

Sai dai ta kara da cewa, tuni ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar ya fara daukan matakan da suka dace don tallafawa ‘yan Najeriyar, tana mai cewa, kungiyoyin agaji na raba abinci, ruwa da magunguna yayin da ake kokarin shawo kan bangarorin da ke fada da su ajiye makamansu.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, ma’aikatar tsaron Pentagon ta Amurka ma na duba zabin da take da shi na kwashe dubban Amurkawa da ke kasar, sai dai Fadar White House ta ce a halin da ake ciki, babu wani shirin na kwashe ‘yan kasarta ta.

“Saboda hali na rashin tabbas da ake fusknta ta fannin tsaro a Khartoum, da kuma rufe filin tashin jirage da aka yi, kada Amurkawa da suke zaune a kasar su sa ran gwamnatin Amurka na da shirin kwashe su a halin yanzu.” Kakakin Majalisar Tsaron Amurka John Kirby ya ce. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here