Home Ilimi Majalisar Wakilai Ta Fito Da Wani Shiri Na Cire Mutum Miliyan 14...

Majalisar Wakilai Ta Fito Da Wani Shiri Na Cire Mutum Miliyan 14 Da Ga Jahilci Da Talauci

219
0
Hon. Aliyu Wurno

Majalisar Wakilai ta sha alwashin ganin an fitar da mutum miliya 14 da ga Jahilci da talauci cikin shekaru hudu masu zuwa karkashin wani tsari na tallafi tare da hadin gwiwa da gwamnatin Taraiya.

Shugaban Kwamitin Samar da Ilimi na Musamman na Majalisar Wakilai, Dan Majalisa Mai Wakiltar Wurno/Rabah da ga Jihar Sokoto, Hon. Ibrahim Almustapha Aliyu ne ya sanar da haka a wata hira da yan jaridu a ofishin sa ranar Litinin.

Hon. Aliyu ya ce Majalisar Wakilai ta lura da irin bukatar da ake da ita na samar da ilimi ga matasa da mata wadanda basa zuwa makaranta tare da samar da aiyukan yi a wani mataki na yakar jahilci da samar da aiyukan yi a kasarnan.

Ya ce wannan dalili ne Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajuddeen Abbas ya ga cancantar Hon. Ibrahim ya nada shi a matsayin shugaban Kwamitin domin a fito da hanyoyi da za su yaki jahilci da talauci a Najeriya baki daya.

Hon. Aliyu ya ce tuni Kwamitin sa ya sami amincewar kungiyoyi wadanda za su tallafa da kudade wadanda za’ayi aiki da su wajen ganin an yaki jahilci da talauci a cikin al’umma baki daya.

Wadan da za su amfana da wannan shiri sun hada da Hukumomi da suke kula Makiyaya wadanda suke yawo da masu kamun kifi, da manoma da almajirai da kuma Hukumar da ke kula da ilimin manya.

Dan Majalisar ya ce koda ya ke shiri ne na kasa baki daya amma yankunan da suka fi yawan mabukata na wannan tallafi su ne za su ci gajiyar mafiyawan wannan tallafi kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa ta sanar.

Hon. Aliyu wanda ya danganta wannan matsala ta rashin tsaro da a ke fuskanta a Arewacin kasarnan da sauran yankuna da cewa jahilci ne ummul aba’isun matsalar. Sabo da haka, idan aka yaki jahilci tun da ga tushe za’a magance barazanar tsaro a kasarnan.

Game da batun yancin kai da Najeriya ta samu 63 da suka wuce a ganin sa basu tafi a banza ba sabo da an samu cigaba a fannoni da dama domin idan an duba baya za a gani cewa an samu cigaba misali harkar ilimi yawan makarantu da jami’o’i sun karu da tituna da sauran aiyuka na cigaba.

Dan Majalisar ya ce duk da cewa an sami cigaba, hakan ba yana nufin babu matsaloli ba. In da ya ce akwai matsala ta tarbiya da rashin bin doka wadanda ya ce akwai bukatar a koma gida a gyara tun da fari.

Hon. Aliyu ya kara da cewa babban abun da ya kamata a bawa fifiko wajen ganin kasarnan ta ci gaba shine bin doka da oda kuma duk wanda baibi ta ba toh! a yi masa hukuncin da ya kamata. Wanda ya ce idan an yi haka abubuwa zasu gyaru a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here