Home Siyasa Majalisar Wakilai Zata Binciki Dalilin Tsaikon Kammala Titin Kano Zuwa Maiduguri, da...

Majalisar Wakilai Zata Binciki Dalilin Tsaikon Kammala Titin Kano Zuwa Maiduguri, da Sauran su

203
0
Hon. Galambi

Majalisar wakilan Najeriya ta yi alkawarin gudanar da bincike domin gano dalilan da suka haifar da tsaiko wajen kammala aikin tagwayen titin Kano Zuwa Maiduguri.

Matakin ya biyo bayan wani kudiri da Hon. Yusuf Shitu Galambi da ke Wakiltar Gwaram da ga Jihar Jigawa ya gabatar domin gudanar  binciken tare da daukar matakin kammala aikin, a zaman Majalisar na ranar Talatar nan.

Da yake gabatar da kudirin  Hon Yusuf Shittu Galambi ya bayyana cewa tun a shekara ta 2006 gwamnatin tarayyar ta bada kwangilar aikin tagwayen  hanyar Kuma aka Kasa shi gida 5, Inda kashin farko na aikin mai nisan kilomita 202 ya kunshi garuruwan kano, Wudil da Gaya daga Jihar Kano da Kuma Shuwarin a cikin Jihar jigawa.

Ya ce Kamfanin Dantata & Sawo aka baiwa kwantiragin kashin farko na aikin hanyar wanda ba a kammala ba yayin da Kawo yanzu an riga an kammala sauran Kashi hudu na aikin hanyar.

Dan Majalisar ya Kuma bayyana damuwarsa kan yadda aka yi watsi da aikin ba tare da wani kwakkwaran bayani duk kuwa kudin da gwamnatin tarayya ta ware domin gudanar da aikin an rigaya an biya shi.

Har ila yau ya nuna damuwarsa dangane yadda ake samun haddura akai akai sakamon rashin kyawun hanyar sannan batagari na anfani da damar wajen aikata laifuffuka ga matafiya akan hanyar.

Ya Kara da cewa rashin kyawun hanyar ya haifan da koma bayan tattalin arziki Inda ya bayyana cewa kammala aiki zai taimaka wajen samar da tsaro ga matafiya  da bunkasa tattalin arzikin al’umomonin dake zaune a yankin.

Da take yanke shawara kan kudirin Majalisar ta ce zata Kafa kwamiti na musanman domin gudanar da bincike akan musabbabin rashin kammala aikin tare da tabbatar da Magance matsaloliin dake Kawo cikas don kammala aikin kana ya gabatar da rahoto cikin makwanni uku.

A wani bangaren kuma Hon. Galambi ya ce Majalisar ta Goma ta sha alwashin bibiyar aiyukan da gwamnatin baya ta yi musamman wadanda su ke da alaka da cinhanci da rashawa.

In da ya kawo misali da badakalar Jirgin Sama mallakar Najeriya wato  “Air Nageria” wanda ya ce akwai rainin hankali a hayo jirgi a kawo Najeriya a matsayin Jirgin Najeriya da ga baya jirgin ya tashi ya koma inda ya fito. Ya ce wannan batu ne da ke bukatar bincikawa kuma dole a hukunta wadanda suke da hannu akan batum.

Ba yan haka ya sake gabatar da batum jinginar da tashoshin jiragen sama na Kano da na Abuja wadanda aka yi kwana shida kafin karshen wa’adin Gwamnatin da ta shude. Wanda ya ce shima batu ne da ya ke bukatar Majalisar ta yi tsatstsauran bincike akan su.

Hon. Galambi ya kara da cewa abun bacin rai shi ne duk wadannan badakala an gudanar da su ne a Gwamnatin da Yan Najeriya su ke da yakinin cewa za ta kamanta gaskiya da rike amanar su.

Sa bo da haka ya ce Majalisa ta 10 za ta bibiyi aiyuka wadan akayi ba bisa ka’ida ba domin hakan ya zama izina ga na baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here