Home Labaru masu ratsa Zuciya MAWALLAFIN JARIDAR VIEWFINDERNG.COM YA MIKA SAKON TA’AZIYA GA DARAKTAN YADA LABARAI NA...

MAWALLAFIN JARIDAR VIEWFINDERNG.COM YA MIKA SAKON TA’AZIYA GA DARAKTAN YADA LABARAI NA GWAMNA GANDUJE

233
0
Aminu Yassar
Aminu Yassar

Shugaban Kamfanin Jaridar Viewfinderng.com, Aliyu Mudi Sulaiman ya mika ta’aziyar jaje a bisa rasuwar Mahaifiyar Daraktan Yada Labara na Gwamnan Jarhar Kano, Alhaji Aminu Kabiru Yassar.

Aliyu Mudi Ya baiyana rasuwar, Hajia Aisha Nagoda a matsayin wani babban rashi ba ga Aminu Yassar Kadai ba;  illa rashine ga al’umar Jahar Kano baki daya.

Shugaban Jaridar yace , Kyawawan halaye da Aminu Yassar yake dasu; wata manuniyace data ke nuna, Marigayiya Aisha ta bashi tarbiyya abar koyi ga al’umar Jahar Kano dama Najeria baki daya.

Yace irin jajircewa da Aminu Yassar yake dashi wajen gaskiya da rikon amana da kuma aiki tukuru; ya nuna irin tarbiyar data bashi. Domin kuwa tarbiya akasarinta daga uwa  tafi karfi kamar yadda addinin Musulunci ya nusar.

Daga karshe yayi fatan Allah ya jikin Hajia Aisha Nagoda, yasa Aljannar Firdausi Makoma , Ya kuma bawa Aminu Yassar da Al’umar Jahar Kano hakuri na wannan babban rashi da akayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here