Home Siyasa CISLAC Ta Bukaci Kungiyar ECOWAS Da Ta Sasanta Da Shugabannin Kasashen Mali,...

CISLAC Ta Bukaci Kungiyar ECOWAS Da Ta Sasanta Da Shugabannin Kasashen Mali, Niger Da Barkina Faso

142
0
CISLAC

Kungiyar nan mai rajin kare  yancin dan adam da Demokradiyyar  wato CISLAC tare da Gamaiyar kungiyoyin da su ke da alaka da ita sun yi kira da Kungiyar ECOWAS da ta nemi Shugabannin kasashen Mali da Niger da Barkina Faso domin su sasanta akan batun  ficewar su da ga Kungiyar.

Shugaban Kungiyar CISLAC Auwal Rafsanjani ne ya yi wannan kiran a taron yan jaridu da kungiyoyin su ka gudanar a birnin taraiya Abuja a ranar Alhamis.

Rafsanjani ya ce dalilin su na yin wannan kira shi ne sun lura da cewa kasancewar kasashen a kungiya guda ya fi alheri fiye da a ce sun kama gaban su ta fannin tattalin arzikin kasa da taimakon juna ta fannin tsaro da zamantakewa da sauran su.

Ya ce a matsayin su na kungiyoyi ma su duba a kan batutuwa da suka shafi jama’a suna duba ne akan alfanun da yak e da tattare da zaman su a matsayin na tsintshiya madaurin ki guda shi ya fi alheri fiye da a ce sun fice da ga cikin kungiyar.

Rafsanjani ya kara da cewa da ga lokacin da aka kafa Kungiyar ECOWAS a shekara ta 1975 kasashen da su ke cikin ta sun amfana da juna ta hanyoyi da dama kuma akwai hadin gwiwa tsakanin su ta fannin tsaro da taimakekeniya a bangarori da dama.

Ya kara da cewa, abu mafi mahimmanci a cikin wannan batu shine wannan ficewa da kasashen sukayi da ga Kungiyar ECOWAS ba bu amincewar mutanen da su ke kasashen Niger da Mali da Barkina Faso. Shugabannin juyin mulkin ne su ka ce sun fice da ga Kungiyar.

Gamaiyar Kungiyoyin sun ce basa goyon bayan juyin mulkin da Shugabannin sojojin su ka yi sabo da haka su na kira da su da su gaggauta shirya zabe domin samar da shugabanci na siyasa wanda zai samar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen.

Dadin dadawa gamaiyar Kungiyoyin sun yi kira da Kungiyar ECOWAS da ta gaggauta cire takunkumin da aka dorawa kasar Niger da sauran kasashen domin irin kuncin rayuwa da takunkumin ya saka jama’ar da suke kasashen musamman mata da yara wadanda ba su su ka yi juyin mulkin ba.

Su ka ce takumkumin ya haramtawa mata da yara da sauran talakawa samun abaubuwa na more rayuwa kamar samun kulawa ta fannin asibiti da samun wutar lantarki da ruwa mai tsafta da sauran abubuwa da dan adam ya ke bukata.

Sa bo da haka, gamaiyar Kungiyoyin sun yi kira ga Kungiyar ECOWAS da ta gaggauta cire takunkumin da aka kakabawa kasar Niger da sauran kasashen domin sa ka takunkumin ya sabawa yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin mambobi na kungiyar.

Gamaiyar Kungiyoyin sun yi kira da Kungiyar ECOWAS da su kasashen uku da su ka fice da ga Kungiyar da su yi duba da irin barazanar tsaro da take addabar kasashen Yammacin Africa wadda sai an hada karfi da karfe wuri guda idan ana so a magance matsalar.

Sabo da haka ne su ka yi kira da Kungiyar ECOWAS da su kasashen da su sasanta da junan su su koma tsintsiya daya madaurinki guda domin hakan yafi alheri ga kasashen da al’umar yankin fiye da a ce kowa ya kama gaban sa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here