Home Ilimi Kasafin Kudi 2024: Ku Dubi FCE, Zaria Da Idon Rahama

Kasafin Kudi 2024: Ku Dubi FCE, Zaria Da Idon Rahama

378
0
FCE Zaria

An yi kira ga Gwamnatin Taraiya da Majalisar Taraiya da su dubi Kwalejin Ilimi ta Zarai wato (FCE,Zaria) da idon rahama su kara mata Kasafin Kudi a shekara ta 2024 domin ceton makarantar da ga kalubalen da ta ke fuskanta.

Shugaban Bangaren Kudi na Kwalejin, Dr. Muhammad Sani Uwaisu ne ya yi wannan kira a lokacin da su ka baiyana a gaban Kwamitin Ilimi na Makarantu na gaba da Sakandare na Majalisar Taraiya don kare kasafin Kudin Kwalejin a wani zama na Hadaka da ya gudana a satin da ya gabata.

Dr. Uwaisu ya ce Kwalejin ta na fuskantar kalubale ma su ya wa wajen gudanar da makarantar kama da ga rashin wadatattun dakunan Karatu da Dakunan bincike (laboratories) da Na’urorin Komfuta da kuma tsadar kayan koyo da koyarwa.

Sabo da haka ne ya roki wadannan hukumomi da su dubi makarantar da idon rahama don kara mata kasafin kudi. “Muna rokon su da su karama mana kasafin kudi. I dan kuma ba za su kara mana ba to, mu na rokon su da kada su rage mana kudaden da muka bukata”. Inji Dr. Uwaisu.

Ya ba da misali da yadda su ke fuskantar tsadar kayan koyo da koyarwa kamar su takardun rubutu, in da ya ce sinkin takarda da su ke saya N8,000 a ba ya, a yanzu a na sayar da shi akan N27,000 a halin yanzu.

Dr. Sani Uwaisu

Uwaisu ya kara da cewa a maimakon amfani da wadannan takardu sun bukaci da a saya ma su Komfuta tun da yanzu abubuwa sun canza. “ Yan zu abubuwa sun canza. I ta kanta JAMB da WAEC da NECO su na shirya jarabawa ne ta hanyar amfani da Komfuta sabo da haka akwai bukatar mu ma mu koma amfani da ita domin tafiya daidai da zamani”. In ji shi.

Ya ce makarantar ta na dauke da dalibai sama da 30,000 wadanda galibin su ya yan talakawa ne sa bo da haka ba za su iya biyan kudin makaranta mai yawa ba domin idan an matsa mu su za su I ya hakura da makarantar. Idan kuma sun hakura za su iya zama barazana ga al’umma musamman a wannan lokaci da a ke fama da barazanar tsaro.

Dr. Uwaisu ya kara da cewa Kwalejin Ilimi ta Zaria tsohuwar makaranta ce wacce shekarun ta na kafawa sun kai 62 kuma ta ya ye manyan mutane a kasarnan. Kamarsu Profesor Mahdi na ABU da tshohon Gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako da marigayi Garba Nadama da Prof. Peter N. Lassa da Sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here