Home Ilimi Kafa Kungiyar Yan Jaridun Yanar Gizo A Kano: Mafita Ga Aikin Jarida...

Kafa Kungiyar Yan Jaridun Yanar Gizo A Kano: Mafita Ga Aikin Jarida A Najeriya

134
0
Online Chp 1

Kafa Kungiyar Yan Jaridun Yanar Gizo wato “NUJ Online Media Chapel” da Gwamnatin jihar Kano, ta yi a ranar Asabar wata manuniya ce  ga inda aikin Jarida ya saka gaba a Najeriya da ma duniya baki daya.

 

Banyi mamaki ganin yadda Gwamnatin Jihar Kano ta yi wuf ta kafa wannan Kungiya ba; wannan ya nu na hangen nesa da Gwamnatin ta yi ganin yadda aikin  Jarida ya  saka gaba.

Online Chp 4

Ko ana so ka ba’a so; ya zama Dole Gwamnatoci da al’ummai dama kamfanoni su rungumi kafafen yada labarai na zamani lura da ganin yadda al’mura su ke faruwa a duniya baki daya.

 

Tuni, kusan dukkanin Jaridu a Najeriya dama Duniya baki daya su ka samar da bangaren da su ke wallafa Jaridar su ta “online”. Wannan ya zamar mu su dole sabo da yadda kasuwar Jaridu ke mutuwa.

Ko da ya har ya zuwa yanzu babu adadin Jaridun da suka rufe su ka koma “Online” amma bincike ya tabbatar cewa da yawa daga Jaridu sun koma “Online” ko kuma bude wani sashe nasa.

Online Chp 3

Karatun Jarida ya koma “Online” sabo da yafi sauri da sauki ga mai karatu. Kafin kace kwabo mai karatu zai sami kararrawar sanarwa ta duk Jaridar da ya kulla alaka da ita wata”subscription”. Bayan haka ba sai ka bayar da kudi ba; abun da kake bukata shi ne ka kasance “online”.

 

Dalilai da su ke kara tabbatarwa cewa Jaridun Yanar Gizo wato “Online newspapers da Magazines” sun sami kwarin gwiwa da ga Gwamnatoci sabo da; da yawa daga cikin su sun nada masu tallafa musu akan harkar yada labarai na “Online” wato “SAs da SSAs”. Gwamnatin Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ce ta fara Nada masu bata shawara akan “Online Media”. Ita Ma Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu bata yi kasa a gwiwa ba ta Nada.

 

Kafa wannan Kungiya ta Yan Jaridun Yanar Gizo wato “Kano Online Media Chapel” da Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi ranar Asabar ya tabbatar da tagomashin da ya yiwa wannan bangare na Yan Jaridu da ya sami goyon bayan Kungiyar Yan Jaridu ta Kasa wato “NUJ”.

Online Chp 2

Kwamared Waiya, yace tabbas kafafen yada labarai a kafafen yanar gizo suna da tasiri a rayuwar al’umma, kuma suna bayar da gudummawa ga cigaban al’umma.

 

Ya hori sabbin shugabannin ƙungiyar dasu zamo masu kokarin kawo sauyi mai kyau a cikin harkokin yaɗa labarai da kuma ciyar da jihar Kano gaba.

 

A nasa jawabin Shugaban kwamitin ƙaddamar da kungiyar wato Alhaji Ahmad Aminu, ya hori masu wallafa labarai a kafafen yanar gizo dasu riƙa tantance labarai kafin akai ga bayyanawa a’lumma, don gudun wallafa labarai na karya ko wanda zasu kawo hargitsi a cikin al’umma.

 

Sannan ya yaba wa Gwamnatin Kano a kokarin da ta bijiro da shi na tsaftace yin magana a kafafen yada labarai.

 

Shi kuwa sabon shugaban kungiyar ƴan jarida masu wallafa labarai a kafafen yanar gizo, Abubakar Abdulqadir Dangambo, ya yi alƙawarin yin aiki tare da ƴan kungiyar tare da kare martabar su, da kuma kokarin daukaka harkar yaɗa labarai a kafafen yanar gizo.

Online Chp 1

Sannan ya yi alƙawarin bayar da gudummawa don samar da cigaban a’lummar jihar Kano baki ɗaya.

Shi ma a jawabinsa, shugaban kungiyar ‘yan jaridu na jihar Kano, Kwamared Suleiman Abdullahi Dederi ya bayyana cewar kaddamar da kungiyar na daya daga cikin manufofinsa domin inganta a’amuran yada labarai a jihar.

Dederi ya kuma bukace su da su hada hannu da uwar kungiyar  a matakin jiha, domin ciyar da kungiyar gaba.

 

Sauran shugabannin da aka rantsar sun haɗar da Khadijah Aminu, a matsayin mataimakiyar shugaba, sai Isyaku Ahmad, a matsayin Sakatare, Zahara’u Nasir, a matsayin mataimakiyar sakatare, sai Abbas Yusha’u, matsayin ma’ajin kuɗi da Zainab Bello, mataimakiyar ma’ajin kuɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here