Home Uncategorized Kungiyar Kabilar Igbo “Renaissance” Ta Ja Hankalin Jama’a Kan Gangamin Batanci Ga...

Kungiyar Kabilar Igbo “Renaissance” Ta Ja Hankalin Jama’a Kan Gangamin Batanci Ga Hope Uzodinma

119
0
Hope Uzodimma 2

An ja hankalin ‘Yan Najeriya cewa su yi watsi da wata kulalliyar da wasu gungun ‘Yansiyasar yankin kudancin Kasar nan ke yi na cin mutunci da bata sunan Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma.

 

Kungiyar ta ja wannan hankali ne cikin wata sanarwar da ta bayar ta bayyana zargin wani mai suna Mr Osita  Okechukwu da zama kanwa uwar gami na wancan gungun ‘Yansiyasa.

 

Daya daga cikin dabarun gangamin shi ne cin mtuncin Gwamna Hope Uzodinma da su ke zargin za su yi amfani da su harda batun zaben fidda gwani na  Gwamnan jihar Edo karkashin jamiyyar APC wanda ba a kammala ba  a matsayin makamin su.

 

Acewar sanarwar da  babban jami’in kungiyar Mr. Nze Nwankwo Njoku, ya rabawa manema labarai a garin Enugu ta bayyana samun bayanan sirri da ke zargin cewa tsohon babban Daraktan Muryar Najeriya Mr. Osita Okechukwu shine Madugun waccan gangami na batunci ga Gwamna Hope Uzudinma,

 

A cewar babban Jami’in kungiyar Nze Nwankwo, wannan yunkuri na da nasaba da rashin samun mukamin Minista da Mr Ositan ya yi tsammanin za a bashi.

Osita

Don haka a cewarsa tsohon Babban Daraktan na Muryar Najeriya , tuni ya yi alwashin yin dukkan mai yuwuwa wajen ganin ya kassara Hope  Uzodinma , cewa irin yadda ya kalubalanci Gwamnan na Imo kan zaban fidda gwani na zaban Gwamna karkashin  Jamiyyar APC, ya tabbatar da cewa yana da mummunar manufa kan Gwamnan jihar ta Imo Hope Uzodinma

 

Kazalika ya lura da cewa  a yayin da wasu ke kalubalantar Gwamnan jihar Imon kan zaben jihar ta  Edo, shi kuwa Mr. Osita kira ya ke yi na a tsige Gwamnan Hope Uzodinm da ga shugabancin kungiyar Gwamnonin Yankin.

 

Sannan ya bayyana cewa ‘Yan kungiyar sa na matukar mamakin yadda ya ke kalubalantar Hope Uzodinma, hakan a cewar sa na alamta lallai sunan sa ya na cikin jerin wadanda ‘Yan siyasar da a kan biya su makudan kudade a koda yaushe don kawai bata sunan Gwamnan jihar ta Imo.

 

Kan haka ma ya jero irin mahimman ayyukan da Hope Ya samawa jama’ar yankin. Alal misali nadin babban Hafsan sojin ruwa da ya ke Tabkin Oguta wanda hakan ya haifar da bunkasar tattalin arzikin Al’ummar Igbo baki daya.

 

Ya ce ko shakka babu wajibin Osita Okechukwu ya fahimci cewa jamiyyar APC a karkashin kulawar Hope Uzodinma, don haka a kwai mutane da dama a yankin da ya kamata a girmama su  don haka bashi da wani kwatanci da Gwamna domin kuwa babban bango ne, don haka batanci day a ke so ya yiwa Gwamna Hope Uzudinma, ba zai yi wani tasiri ba ko kadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here