Home Noma da Kiwo Za Mu Tabbatar Da Cewa An Raba Taki Miliyan 2 Da Saura...

Za Mu Tabbatar Da Cewa An Raba Taki Miliyan 2 Da Saura Kayan Noma Ga Manoma Na Gaskiya – Hon. Ka’oje

122
0
Hon. Ka'oje 3

Majalisar Taraiya ta ce a shirye  ta ke ta ga ta yi aiki da Gwamnatin Taraiya wajen ganin an rabawa Yan Najeriya taki miliyan biyu da dubu 150  ga manoma na gaskiya a wani mataki na wadata kasa da abinci.

Shugaban Kwamitin Noma da wadata Kasa da abinci na Majalisar Wakilai Hon. Bello Ka’ole ne ya sanar da haka a hirar sa da Yan Jaridu jimkadan da kammala wani zama na hadaka da Majalisar ta yi da Ministocin Noma a jiya Talata.
Ya ce dalilin  su na ganawa da Ministocin shine domin cigaba da bibiya na matakai da Gwamnatin Taraiya ta ke dauka na warware matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a kasarnan.
Hon. Ka’oje ya kara da cewa Takin da za a rabawa manoma da iri da magain feshi  an kimanta  shi zai kai kimanin na Naiara  dubu 450 da za a ba da su kyauta ne amma Gwamnatin ta na bukatar buhu 2 na abin da manomi ya noma domin ajiyewa gudun ko ta kwana.
Har ila yau ya ce shi kuma kayan  abincin da za a raba wato Masara da Dawa da Garin Kwaki ne kimanin ton dubu 42 za a bada shi ne kyauta ga mutane masu rauni a cikin al’umma.
Dadin dadawa, Hon. Ka’oje ya  ce Gwamnatin Taraiya ta shiga wata Yarjejeniya da Bankin Cigaban Africa da kuma wani Kamfanin hada motocin Noma mai suna Gendar don samar da matoci Noma kimani dubu 8 daga nan zuwa shekara ta 2027.
Amma ya kara da cewa za a fara da guda 2000 a cikin wannan shekarar sannan daga bisani za a cigaba da hada motion anan Najeriya.
IMG 20240319 WA0140
Tunda  fari Shugaban Kwamitin Noma na Majalisar Datttawa,  Sanata Salihu Mustapha a yayin karin haske ga Yan Jaridu ya ce wannan tuntuba da su ke yi na daga cokin aikin su a matsayin su na Wakilan jama’a don sa ido su tabbatar da cewa Gwamnati ta na yin abun da ya kamata.
Ya ce akwai hadin gwiwa tsakanin Majalisar Taraiya da Gwamnatin Taraiya da Jami’an Tsaro wajen ganin an magance barazanar tsaro da ta addabi wasu Yankuna a wani mataki na samar da kyakkyawan yanayi don samar da abinci wadatacce a Kasarnan.
Sanata Salihu ya ce Majalisar Taraiya ta gamsu da matakai da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke dauka wajen ganin an samar da wadatatcen abincin a kasarnan.
Da ga Karshe Dan Majalisar ya nuna gamsuwar su na yadda Ministocin Noma su ke bawa Majalisar Taraiya hadin kai ta hanyar amsa kirinta a duk lokacin da su ka kira su.
Sannan sun  yi alkawarin ba su hadin kai wajen yin aiki tare don ganin an samawa Yan Najeriya sauki da su ke bukata cikin sauri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here