Home Noma da Kiwo Wadata Kasa Da Abinci: An Bukaci Gwamnatin Taraiya Da Ta Gaggauta Raba...

Wadata Kasa Da Abinci: An Bukaci Gwamnatin Taraiya Da Ta Gaggauta Raba Tallafin Kayan Noma A Arewa Ta Tsakiya

213
0
Hon. Saba

Majalisar Wakilai ta bukaci Ma’aikatar Noma ta Gwamnatin Taraiya da ta gaggautta fara raba tallafin kayan Noma a Yankin Arewa ta tsakiya a wani mataki na bawa manoma dama fara shuka don gudanar da noman rani a Yankin ba tare da bata lokaci ba.

Majalisar ta gabatar da wannan bukata ne ranar Laraba sakamakon wani Kuduri na gaggawa da Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Edu da Moro da Patigi da ga Jihar Kwara, Hon. Ahmed Adamu Saba ya gabatar a zauren Majalisar.

Ya ce dalilin sa na gabatar da wannan bukata ita ce, noma shi ne kashin bayan al’umarsa kuma Noman Rani ana fara shi ne a watan Nuwamba sabo da haka idan ba a raba tallafin da Gwamnatin Taraiya ta ce zata bawa manoma ba a wannan lokaci za a samu matsala a wannan shekara.

Hon. Saba, ya ce a matsayin sa na Dan Majalisar Taraiya ya san cewa sun amince da wannan tallafi a cikin kwarya-kwaryar kasafin kudi na 2023; kuma ga shi shekara tana karewa sabo da haka bai ga dalili ba na jinkiri da ake samu na rabawa manoma wannan tallafi da aka ce za a ba su.

Ya ce a Gwamnatin da ta shude, an rabawa mutanen sa tallafin Noma kuma tallafin ya taimaka wajen samawa kasarnan abinci tare da inganta rayuwar manoma in da da yawa da ga cikin su sun je aikin Hajji sun gina gidaje kuma sun sayi motoci sabo da haka raba wannan tallafi zai kara inganta rayuwar al’umar sa.

Dan Majalisar ya ce Majalisar Wakilai ta umarci Ma’aikatar Noma ta Kasa da ta gaggauta raba kayan Noman rani da Iri da takin zamani akan lokaci sabo da a bawa Manoma dama su fara shirye-shirye tun kafin lokaci ya kure mu su.

Ya tunatar da Majalisar cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da Dokar ta Baci a kan Harkar Noma a wani mataki na wadata Kasa da abinci. Kuma Jihohin Arewa ta Tsakiya su ne kashin bayan Noma a Najeriya sabo da haka ya zama wajibi a tallafa mu su idan ana so a yaki talauci da tsadar rayuwa da kuma tashin gwauron zabi da farashin abinci ya keyi a kasarnan.

Hon. Saba ya kara da cewa, ambaliyar ruwa da aka samu a daminar bana ya kawo nakasu a noman da aka yi. Sabo da haka, Noman Rani da za a yi shi ne zai tallafa wajen magance asarar da aka yi a daminar da ta wuce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here