Home Siyasa Mun Gamsu Da Hujjojin Tinubu Na Ciyo Bashi – Majalisar Dattawa

Mun Gamsu Da Hujjojin Tinubu Na Ciyo Bashi – Majalisar Dattawa

191
0
SEN. HANGA3

Majalisar Dattawa ta ce ta gamsu da du ka hujjojin da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta gabatar mata na ciyo bashin Dalar Amurka Biliyan 7.8 da Uro miliyan 100 a satin da ya gabata.

Dan Majalisar Taraiyan Mai wakiltar Kano ta Tsakiya Sanata Rufa’I Sani Hanga ya tabbatar da haka a hirarsa da Yanjaridu a ofishin sa dake Majalisar Taraiyar Abuja a ranar Alhamis da ta gabata.

Sanata Hanga ya ceMajalisar ta yi nazari akan du ka hujjojin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata na dalilan sa na ciyo bashin kuma sun gamsu da duka hujjojin sabo da haka ne suka amince da a ciyo bashin.

Dan Majalisar ya ce sun kulle kofa su isu kuma sun gamsar da kansu sannan sun yi alkawarin ganin cewa idan an ciyo bashin za su saka ido wajen ganin an aiwatar da duk abubuwan da aka ce za ayi da su.

Sanata Hanga ya kara da cewa “ kowacce kasa ta duniya ta na cin bashi. Kasashe irin su Amurka da Ingila da sauransu suma suna cin bashi. Kai Aliko Dangote ma wanda yafi kowa kudi a Africa shima yana cin bashi. Abun dubawa anan shine idan an ciyo bashin me za ayi da shi? Idan abu mai kyau ne za ayi da shi ba matsala”.

Shima Sanata Ali Ndume, Bulaliyar Majalisar ta Dattawa ya nuna gamsuwarsa da hujjojin da Shugaban Kasa Ahmed Tinubu ya gabatar musu na ciyo bashin in da ya ce ba  laifi bane ciyo bashi sai dai bashin ayi amfani da shi wajen aiwatar da aiyuka da za su kawo cigaban kasa.

SEN. NDUME 3

Game da kasafin kudi da Majalisar ta amince da shi na sama da Naira Tiriliyan biyu Sanata Ndume ya ce sun amince da shine sabo da mafi yawan kasafin kudin za ayi amfani da s hi ne wajen inganta rayuwar Yan Najeriya ne.

Ya ce daga cikin kudin za ayi amfani da shi ne wajen bayar da tallafi ga talakawa mutum miliyan 15 da Karin albashin ma’aita da kuma samar dakarin yawan sojoji da kayan aiki da Karin albashin Yansanda da harkar noma da gyara hanyoyin kasarnan da sauran su.

Sanata Ali Ndume ya ce cece kuce da ake yi akan sayen motoci ga fadar shugaban kasa Naira Biliyan 28 kawai kuma akwai bukatar motoci a gidan ne kuma ba Bola Ahmed Tinubu za a sayawa ba, fadar za’a sayawa koda ya tafi za a cigaba da amfani da su a fadar.

Sanatan ya yi alkawarin cewa Majalisar Dattawa za ta saka ido wajen ganin aiyukan da aka ce za a yi da kudaden an yi amfani da su kamar yadda ya kamata idan kuma ba a yi ba za su sanar da Yan Najeriya rahoton binciken su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here