Home Zirga zirga Najeriya Zata Bada Goyon Baya Wajen Sufurin Jiragen Sama A Afirka

Najeriya Zata Bada Goyon Baya Wajen Sufurin Jiragen Sama A Afirka

177
0

Gwamnatin Najeriya tayi alkawarin bada goyon baya domin kaddamar da haddadiyar Kasuwar sufurin Afirka ta Sama (SAATM) da ake sa ran zai taimaka wajen kasuwancin bunkasa hada-hadar jiragen sama a nahiyar Afirka daga kaso 14.5% zuwa kaso 30% zuwa shekarar 2025.

 

Domin gaggauta aikin kaddamar da shirin na SAATM, hukumar dake kula da harkokin kamfanonin jiragen sama na Najeriya NCAA ta yi wani gangami wanda ya kunshi jihohi 20 da aka gano irin rawar da zasu iya takawa wajen gaggauta kaddamar da shirin.

Ministan Hada-hadar jiragen Najeriya Sanata Hadi Sirika ne ya yi wannan alkawarin a Abuja , babban birnin Najeriyar a yayin da hukumar matuka jirgin Najeriya sukayi gangamin.

Ministan, wanda babban sakataren ma’aikatar harkokin jiragen na Najeriya Dr. Emmanuel Meribole ya wakilta ya ce, kasuwar jiragen sama a kasashen yankin Sahel na Afirka yana bayyana waagegen gibin da ke akwai a kudanci da gabashin nahiyyar Afirka. A cewarsa, duk da cewa kasuwar hada-hadar jirage tana bunkasa a Afirka, jiragen kasashe ‘yan kalilan ne suka mamaye kasuwannin cikin gida Afirka da kasashen waje.

Sannan, ya kara da cewa, a yankin tsakiya da yammacin Afirka, harkokin zirga-zirgar jiragen sama yana fuskantar koma baya ko kuma ma ace karkokin sun tsaya bisa la’akari da rushewar jiragen kasashe da kuma wasu tsiraru dake mallakin ‘yan kasuwa a yankin.

Ministan ya sheda mahimman cigaba da nasarorin da wasu jihohi da kamfanoni suka cimma a yankin musamman ma ita hukumar harkokin hada-hadar jiragen sama na Afirka bisa kokarinta na ganin cewa ta kaddamar da jadawalin tsarin ayyukan hada-hadar jirage na kungiyar hada-hadar jiragen sama na kasa da kasa SARPs.

 

Babban burin hukumar harkokin sufurin jiragen saman shine yin aiki tare da masu ruwa da tsaki a fannin na ganin an inganta ‘yancin zirga-zirgar shige da fice a Afirka daga inda ake yanzu da kasu 14.5% cikin dari zuwa kaso 30 zuwa shekara ta 2025.

Gwamnatin Tarayyar Najeriyya ta jaddada goyon bayan ta akan dukanin wasu dokoki da shirye-shiryen da zasu taimaka wajen ganin an kaddamar da wannan shirin samar da kasuwar bai daya na hada-hadar jiragen saman Afirka SAAT. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here