Home Siyasa Yadda Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa

Yadda Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa

167
0
Ganduje da Tinubu

Bayan da tsohon shugaban jam’iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa a watan Yulin day a gabata, Jam’iyar APC ta sake zabar Shugabannin Jam’iyar a ranar Alhamis.

Jam’iyyar ta APC mai mulki a Najeriya, ta zabi tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon shugabanta.

APC ta zabi Ganduje ne a babban taronta da aka gudanar yau Alhamis a Abuja.

Kazalika jam’iyyar ta zabi Ajibola Bashir a matsayin sabon babban sakatarenta.

Zabe wanda aka gudanar a Otel din Transcorp da ke Abuja ya sami halartar Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da gwamnoni da Yan Majalisar Taraiya. Sai dai Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron bad a shi da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbanjo.

Amma Tsohon Mai Magana da Yawun Tshohon Shugaban Kasar, Malam Garba Shehu y ace dalilin day a sa Buhari bai halarci taron ba shine ya riga ya yi wa wasu alkawari na halartar taron su kafin a sanar da shi na Jam;iyar APC shi ne ya sa bai halarta ba.

A tsakiyar watan Yulin da ya gabata tsohon shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa wanda aka zaba a watan Maris din 2022.

Bashir ya maye gurbin Sanata Iyiola Omisore wanda shi ma ya ajiye aikinsa rana daya da Adamu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here