Home Tsaro 2026: Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Ta Sha Alwashin Tsaurara Tsaro A...

2026: Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Ta Sha Alwashin Tsaurara Tsaro A Bikin Sabuwar Shekara

46
0
CP Bakori

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano tace zata tsaurara tsaro a wuraren ibada, wuraren shakatawa da sauran muhimman wuraren taruwar jama’a, tare da sintiri na sa’o’i ashirin da huɗu, kula da zirga-zirgar ababen hawa da inganta tattara bayanan sirri a faɗin jihar.

 

Haka kuma, rundunar ta gargadi jama’a da su guji tuki ba bisa ka’ida ba, wuce gona da iri a gudu, tukin yara ƙanana da kuma hawan doki ba tare da izini ba, tare da haramta amfani da bangers da kuma harba wutar biki. Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su kasance masu sa ido tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa, tana mai yi wa al’ummar Kano fatan shiga sabuwar shekarar 2026 lafiya da zaman lafiya.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma gabanin bikin sabuwar shekara. Rundunar ta bayyana cewa an ɗauki matakan tsaro na musamman a sassan jihar domin tabbatar da zaman lafiya yayin bukukuwan ƙarshen shekara.

 

Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Laraba. Sanarwar ta ce Kwamishinan ya gudanar da taron bita da kwamandojin ayyuka a ranar 29 ga Disamba, 2025, inda ya yaba musu kan nasarar da aka samu wajen tsaron bukukuwan Kirsimeti, tare da umartar ƙara yawan sintiri da ayyukan tsaro bisa bayanan sirri.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here