Home Uncategorized Babu Sauyi A Najeriya Da Ghana Kan Cin Hanci Da Rashawa A...

Babu Sauyi A Najeriya Da Ghana Kan Cin Hanci Da Rashawa A 2022 – Transparency International

168
0

Wani rahoto kan cin hanci da rashawa da ƙungiyar Transparency International (TI) ta fitar, ya ce har yanzu babu wani sauyi da aka samu a Najeriya da Ghana game da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa mai tattara bayanai kan matsalar cin hanci da rashawa a duniya Transaparency International, ta ce duk da samun ci gaba akan matsayin da take wato daga 154 cikin jerin kasashe 180 a shekarar 2021 zuwa matsayi na 150 a shekarar 2022, Najeriya ba ta samu ci gaba ba cikin makinda ta samu a 2022 wato matsayi na 24 cikin 100 da take har yanzu.

Ita kuwa kasar Ghana da ta zo matsayi na 72 cikin jerin kasashen 180 bata samu wani ci gaba ba akokarintata na yaki da cin hanci da rashawa, haka zalika bata samu koma baya ba.

Sai dai kuwa wasu kasashen Afrika ta yamma kamar Jamuhiyar Nijar ta samu maki 32 cikin 100 kuma ta na matsayi na 123 cikin kasashe 180.

Kazalika kasar Kamaru ta samu maki 26 cikin 100 inda take matsayi na 142.

Usama Armiyau masanin tattalin arzki kana mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a Afrika, na ganin zuba kudade wuraren da basu dace ba, shine kan gaba cikin abubuwan da ke haifar da wannan matsala.

Haka kuma ya kara da cewa idan aka sa dokoki kan dukiyoyin da aka sace aka adana a ƙasashen waje, ana iya ganin sauyi mai kyau a yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here