Home Muhalli Ya Kamata Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakan Gaggawa Kan Bude Madatsar Ruwa...

Ya Kamata Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakan Gaggawa Kan Bude Madatsar Ruwa Ta Lagdo – Masana

184
0
Dam = Lagdo

Masu fashin baki a Najeriya sun yi kira ga gwamnatin kasar da dauki kwarararn matakai a sha’anin sako ruwa da ake yi daga madatsar ruwan Lagdo da ke kasar Kamaru, wanda ke haifar da mummunar illa a Najeriyar.

Mahukuntan Najeriya sun sanar da cewa sun sami sanarwar za’a sako ruwa daga madatsar ruwa ta Lagdo da ke kasar Kamaru ne kimanin kwanaki bakwai bayan an riga an bude madatsar ruwan lamarin da suke ganin cewa wasikar gargadin ta zo a kurarren lokaci.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA tace ta sami wata takardar diflomasiyya daga ofishin jakadancin kasar Kamaru cewa mahukuntan kasar ta Kamaru sun yanke shawarar bude mashedar madatsar ruwan Lagdo sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi a yankin Arewacin Kamaru, wanda ya sa madatsar ruwan ta cika ta batse.

Tuni dai ‘yan Najeriya musamman ma manoma da mazauna yankunan da ke kewaye da rafi, magudanun ruwa da koguna suka fara tofa albarkacin bakinsu a game da matakin na kasar Kamaru.

Da dama suna cewa ba’a kyautawa kasarsu ba inda wani manomi daga jihar Bauchi, Haruna Yakubu ya ce kasar Kamaru ta saba ka’ida amma yanzu aiki ya koma kan gwamnatin Najeriya ta dauki matakan gaggawa don kawar da ilollin da matakin zai iya jawo wa al’ummar kasar.

Dr. Muhammad Goje shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe, ya ce tuni gwamnatin jiharsa ta dauki matakin wayar da kan al’umma musamman wadanda ke kusa da yankunan da ambaliyar ruwa ya fi shafa tare da fara shirya wuraren da za’a tsugunar da mutane na wucin gadi don kaucewa muggan illoli da bude madatsar ruwa ka iya jawowa.

A wani bangare kuma masani a fannin sha’anin alkinta muhalli kuma jigo a gidauniyar Green Habitat, Injiniya Sadiq Abubakar Gulma, ya ce idan ba’a sauya yanayin daukar matakan da aka saba dauka ba a kan batun bude madatsar ruwa a Kamaru, za’a ci gaba da fuskantar matsaloli. Amma ya kamata gwamnati ta gina hanyoyin ruwa a bayan garuruwa da suka fi fama da matsalolin ambaliya da dai sauransu.

Masana a kan sha’anin mahalli dai sun ce rashin aiwatar da shawarwarin kwamitocin da gwamnati ta kafa bayan bala’o’in ambaliyar ruwa a shekarar 2012 da 2022 don gudanar da bincike da samar da cikakkun tsare-tsaren hana sake afkuwa hakan ne musababbin ibtila’in ambaliyar ruwa da ake gani kuma dole ne gwamnati ta aiwatar da wadannan shawarwarin don kawo mafita.

Duk kokarin jin ta bakin ofishin jakancin Kamaru a Najeriya bayan ziyara da aika wasiaka kan matakin da mahukuntan kasar suka dauka a yayin hada wannan rahoton dai ya ci tura.(Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here