Home Siyasa Jami’in Mu Ya Yi Riga-malam Masallaci Wurin Bayyana Sakamako A Adamawa-INEC

Jami’in Mu Ya Yi Riga-malam Masallaci Wurin Bayyana Sakamako A Adamawa-INEC

181
0

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce kwamishinan zabenta a Adamawa ya yi gaggawar fadin sakamakon zabe ba tare da kammala tattara sakamakon ba.

Kwamishinan dai a cikin hargowar wadanda ke hamayya da sakamakon, ya ayyana A’isha Binani ta APC a matsayin wacce ta lashe zaben.

INEC ta ce don haka ta dakatar da ayyana sakamakon da gayyatar duk jami’an zaben don taro a Abuja da zummar sake komawa don cigaba da aikin tattara sakamakon.

Kwamishinan labaru da ilmantar da masu kada kuri’a na hukumar Festus Okoye ke cewa jami’in zaben ya sanar da sakamakon ba tare da ya na da hurumin yin hakan ba don haka har yanzu da sauran magana kenan kan sakamakon.

Okoye ya kara da cewa tuni kwamishinan zaben ya iso Abuja don yin taro da shi a Talatar nan kuma babban jami’in zabe ne ke da hurumin sanar da sakamakon.

Kwamishinan ya ce hakika za a koma Adamawa don cigaba da tattara ainihin sakamakon don ayyana wanda ya lashe zaben kuma hakan mai yiwuwa ne a fara daga Talatar nan.

Tuni dattawa da masu fashin bakin siyasa ke bukatar al’ummar Adamawa su jira mataki daga hukumar zaben da kaucewa duk wani yanayin da zai kawo hargitsi.

Dr. Mahdi Abba wanda malami a jami’ar Modibbo Adama na daga cikin wadanda ke bin sakamakon zaben da ba da shawarar sauraron hukunci daga hukumar zaben ta kasa.

Aisha Binani ta APC wacce a yanzu haka ‘yar majalisar dattawa ce na kalubalantar gwamnan Adamawa Umar Fintiri na PDP a zaben da ya ja zare da daukar hankalin jam’ar ciki da wajen Najeriya. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here