Home Siyasa Yadda Abba Kabir Yusuf ya lashe zaben gwamnan jihar Kano

Yadda Abba Kabir Yusuf ya lashe zaben gwamnan jihar Kano

208
0

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.

Abba Kabir, wanda ake yi wa laƙabi da Abba Gida-gida ya samu nasara ne a kan abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC mai mulki Nasiru Yusuf Gawuna.

Gawuna shi ne mataimakin gwmnan jihar Kano.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan Kano Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.

Sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar PDP ce ta zo ta uku, inda Sadik Wali ya samu ƙuri’u 15,957, sai kuma Sha’aban Ibrahim Sharaɗa na jam’iyyar ADP ya samu ƙuri’u 9,402.

A shekarar 2019 ne Abba Kabir ya fara takarar gwamnan kano inda ya yi takara da Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC.

Jam’iyyar NNPP ce ta lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, ta kuma lashe biyu cikin uku na kujerun sanatocin Kano, sannan da mafi yawancin kujerun majalisar wakilai daga jihar ta Kano.

‘Dokar hana fita’

Gwamnatin jihar Kano ta kakaba dokar hana zirga-zirga a fadin jihar na tsawon awa 24.

A wani bayani da ya fitar, mai magana da yawun gwamnan jihar Muhammad Garba, ya ce dokar ta fara aiki ne daga karfe takwas na safiyar Litinin zuwa karfe takwas na safiyar Talata.

An dai sanya dokar ce jim kadan gabanin sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar, wanda ya ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya yi nasara.

Kakaba wannan doka na da alaka da gudun tashin hankali da ka iya barkewa bayan an aiyana wanda yaci zaben.

Ko da yake binciken Viewfinder hausa ya ga magoya bayan Jam’iyar NNPP na ta murna tun ranar Lahadi da daddare. Wannan ya na alaka wata kila da irin sakamakon da suke samu daga kananan hukumomin da ke jihar.

A yayin da hukumar INEC ta aiyana Abba Kabir a matsayin wanda ya samu nasarar wannan zabe, magoya bayansa sun bazama kan titunan Kano suna nuna farin cikinsu da jin dadi ta hanyar guje guje da Babura da motoci da kide=kide.

Sai dai a wasu wuraren an sami wasu magoya bayan jam’iyar ta NNPP suna yage allon tallace tallace na jam’iyun adawa musamman na jam’iyar APC suna cinna musu wuta. A wasu wuraren ma rahotanni sunce an fasa motocin wadanda ake zargi basa goyon bayan su.

Ko da yake jami’an tsaro sun rinka jefa hayaki mai sanya hawaye a gurare da akayi dandazo domin kwantar da tarzoma a jihar ta Kano.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here