Home Mulki Majalisar Dattawa Ta Yaba da Kokarin Gwamnatin Buhari A Shekaru Takwas

Majalisar Dattawa Ta Yaba da Kokarin Gwamnatin Buhari A Shekaru Takwas

233
0

Majalisar Dattawa tace Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Bauhari tayi rawar gani a shekaru takwas da ta shafe akan mulkin Najeriya duk da korafe korafe da mutane keyi kan gwamnatin.

Shugaban Kwamitin Zabe kuma tsohon Shugaban Kwamitin Aiyuka na Majalisar Dattawa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ne ya furta hakan a hirar sa da yan jaridu a ofishin sa dake Majalisar a Abuja.

Yace mutane suna mantawa ne da yadda Shugaba Muhammadu Buhari ne ya karbi kasarnan musamman ta fannin tsaro shi yasa suke kushe irin kokarin da gwamnatin sa tayi a shekaru takwas da suka wuce.

“ Sanin kowa ne lokacin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta hau mulki yan Boko Haram suna cin Karen su ba babbaka a jahohi da dama a Arewacin kasarnan musamman a Jihar Borno inda suke rike da kusan dukkan kananan hukumomi dake Jihar “

Yace Kano da Jihohi da dama a Arewacin kasarnan sun fuskanci kalu bane na Boko Haram inda suka salwantar da rayuka da dukiyoyin al’umma tare da hana su walwala ta yau da kullum amma a halin yanzu abun ya zama tarihi.

Sanata Gaya yace, ko da ya ke tarwatsa yan Boko Haram ya haifar da wata matsalar tsaro ta garkuwa da mutane amma ita ma a halin yanzu ta kusan zama tarihi domin kuwa an sami sauki da yawa.

Shugaban Kwamitin Zaben yace, Majalisar Dattawa ta tara ta samu kyakkyawar dangantaka da Fadar Shugaban Kasa wanda hakan ya kawo nasarori wajen aiwatar da manyan aiyuka a kasarnan kamar samar da manyan tituna a kasarnan irin su titin Abuja zuwa Kano da gadar 2nd Niger Bridge da samar da layukan Dogo da samar da bututun iskar Gas daga Kudu zuwa Kano da akeyi a halin yanzu.

Ya kara da cewa, a matsayin sa na tsohon shugaban Kwamitin Aiyuka shi ganau ne ba jiyau ba wajen ganin irin aiyuka da Gwamnatin Buhari tayi irin su sabunta wuraren sauka da tashi na tashoshin Jiragen Sama dake kasarnan kamar na Kano da Fatakwal da Legas da Abuja abun a yabawa Shugaba Buhari ne.

A fannin noma ma yace, Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi rawar gani wajen maida mutane gona domin kuwa noman shinkafa da akeyi a kasarnan ya bunkasa tattalin arzikin kasarnan da dubban Yan Kasarnan.

Sanata Kabiru Gaya ya kara da cewa, wannan matatar Mai da Aliko Dangote ya gina ta samu ne sakamakon goyon baya da tallafin Gwamnatin Muhammadu. Yace Matatar zata samar da aiyuka ga dubunnan Yan Najeriya tare da bunkasa tattalin arzikin Najeriya da Yan Najeriya ta fannoni da dama.

Yace, samar da matatar na nufin dakatar da kwasar arzikin kasarnan zuwa kasashen waje domin tace danyen Mai. Zai kuma kawo wa kasarnan kudaden shiga ta hanyar sayar da Mai da dangogin su ga kasashen duniya.

Daga Karshe Sanata Gaya ya yaba da kokarin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan wanda yace a bisa jagorancin sa ne Majalisar ta kafa tarihi na samar da Kudure Kadure mafi yawa sama da dukkan Majalisu da aka yi tun da aka fara siyasa a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here