Home Uncategorized WHO ta ce ayyuka sun tsaya cak a babban asibitin Gaza

WHO ta ce ayyuka sun tsaya cak a babban asibitin Gaza

117
0
Gaza Harin Asibiti

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO) ta ce komai ya tsaya cak a asibitn Al-Shifa na Birnin Gaza, inda dubban mutane su ka maƙalle.

Dr Marwan Abu Saada, wani likita ne a Gaza, ya kuma tabbatar cewa jariri na uku ya mutu, daga cikin waɗanda yake jinya.

Hamas ta yi watsi da matsayar Isra’ila da ke cewa mayaƙan Hamas ɗin suna da ramukan ƙarƙashin ƙasa da suke ɓoyewa.

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta soki Hamas saboda fakewa a asibiti, yayin da ake ci gaba da gwabza fada, tare da neman Isra’ila ta kaucewa kisan fararen hula a hare-haren ta.

Tun da farko dai wasu rahotannin sun ce Hamas ta dakatar da duk wata tattunawar sulhu, kuma hakan na nufin mutanen da take tsare da su suna cikin mawuyacin hali.

Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ya amince da kai kayan agaji Gaza, ciki har da fetir da ma sauran kayan buƙata, kuma tuni Hamas ta ce bata buƙatar tallafin.

A hirar sa da BBC daga Ramallah dake gaɓar yamma da kogin Jordan Dr Mustapha Barghouti, ya bayyana halin da ake ciki a kan yaƙin a yanzu.

Ya ce “Aniyar su ita ce kawar da Falasɗinawa daga doron ƙasa. Kawo yanzu sun kashe fararen hula dubu sha ɗaya, cikin su kuma harda ƙarnanan yara dubu biyar. Wannan laifin yaƙi ne, aikata kisan gillah da neman kawar da wata al’umma daga doron ƙasa har abada.”

Hukumomin Gaza sun ce akwai dubban mutane da suka makale a asibitin Al-shifa, yayin da da dama cikin waɗanɗa suka samu tsallakewa zuwa wasu wuraren na daban ke cikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here