Home Addini Yadda Rikicin Sudan Ya Yi Sanadin Ragewa A lhazai Kudin Guzuri

Yadda Rikicin Sudan Ya Yi Sanadin Ragewa A lhazai Kudin Guzuri

137
0

Rikicin Sudan da ya sa aka rufe sararin samaniya ya janyo karin kudin kujerar aikin Hajji a Najeriya da dala 250, don dole a zagaya ta hanya mai nisa da hakan ya sa kamfanonin jiragen da za su yi jigilar maniyyatan suka bukaci karin kudi.

 

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta shiga ta ba da tallafin kashi 65 na karin kudin da hakan ka iya saukakawa alhazan yawan kudin da za su yi kari.

Kwamishinan ayyuka da lasisi na hukumar Alhazai ta kasa NAHCON Abdullahi Magaji Hardawa, ya ce bayan shawartar hukumar da ofishin mai bawa shugaba Buhari shawara kan harkokin tsaro tare da bayyana irin hadarin dake cikin bin sararin samaniyar kasar Sudan ya sa dole akayi shawarar hanyoyin da za’a bi don jigilar maniyatan zuwa kasa mai tsarki.

Kwamishinan ya ce bayan gwamnati da hukumar alhazai NAHCON sun bada tallafi akan kudin da kamfanonin suka bukaci a kara, sai kuma ko wane maniyaci ya kara dala 100 don cikon karin.

Abdulllahi Magaji ya ci gaba da cewa hukumar tayi la’akari da cewa idan aka bukaci dala 100 daga ko wane maniyyaci zai zama abun damuwa, don hakan yasa akayi shawarar cire kudin daga kudin guzurin maniyyatan.

Hakan na nufin hukumar zata rage kudin guzurin alhazan daga dala 800 zuwa 700 wanda na nuna alhazan zasu biya kudin amma ba kai tsaye ba.

Hardawa ya ce idan Allah yasa lamura suka sauya hanya ta bude kai tsaye ta Sudan za’a dawo kuma za’a dawowa da alhazan dala 50.

Za’a fara jigilar maniyata hajjin na bana daga ranar 25 ga watan nan. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here