Home Mai da Iskar Gas Dalilin Da Ya Sa Farashin Mai Ya Fadi A Duniya

Dalilin Da Ya Sa Farashin Mai Ya Fadi A Duniya

71
0
Fuel drops

Farashin mai ya yi ƙasa a kasuwannin duniya bayan da Isara’ila ta mayar da martani hare-hare a ƙasar Iran ranar Asabar. Da farko dai an samu hauhawar farashin man ne saboda fargabar da ake da ita na cewa Isra’ila za ta iya kai hare-hare kan wuraren samar da man fetur na Iran.

Sai dai kuma bayan hare-haren martanin, sai farashin man ya sauka da kashi huɗu cikin ɗari.

Tun da farko, Iran, ta yi alƙawarin mayar da wani martanin wanda a cewarta daidai da wanda ya dace na hare-haren da Isra’ilar ta kai kan sansanin soji da cibiyoyin samar da makamai na ƙasar.

Zaman tankiya a tsakanin ƙasashen biyu ya ƙara tsananta ne bayan Iran ta harba makamai a Isra’ila a matsayin martani da kashe shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah da Isra’ilar ta yi, wanda tun a lokacin Isra’ilar ta ƙuduri aniyar mayar da martani.

Tun a lokacin ne Amurka take ta nanata matsayarta ta cewa ba ta so Isara’ila ta kai hari a sansanonin nukiliyar Iran. (BBC Hausa).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here