Home Addini Yadda Aikin Sabunta Masallacin Zazzau Ya Kankama

Yadda Aikin Sabunta Masallacin Zazzau Ya Kankama

53
0
IMG 20230928 WA0059
DOMIN fara aikin sabunta Babban Masallacin Jumma’a na Sarkin Zazzau Abdulkarim wanda ke Kofar Fadan Zazzau da ranan yau an fara rushe Masallacin wanda ya kasance a rufe tun watan Augustan shekarar da ta wuce bayan fafuwan wani bangare na masallacin wanda yai sanadiyyar rasa rayukan Mutum Takwas gami da sakun raunikan wasu masallata a cikin Masallacin.
Idan za a iya tunawa da aukuwan wannan hatsari Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ya kafa kwakarran kwamitin Masana domin samar da sabun Masallacin. Wannan kwamiti dai ya kasance ne a bisa jagorancin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma Sardaunan Zazzau, Arch.  Muhammadu Namadi Sambo.
A watan Oktoba na shekarar da ta gabata a Babban Dakin Taro na Shehu ‘Yar Adua wanda ke Birnin Tarayya Abuja an kaddamar da Gidauniya domin sabunta wannan Masallaci. A lokacin an tara Naira Biliyan Uku domin aikin inda Babban Mai Kaddamarwan kuma Shugaban rukunin Kamfanonin BUA, Alhaji Abdus-samad Rabi’u ya bada gudumuwar Naira Biliyan Biyu.
Har yanzun dai, kofar bayar da gudunmuwa domin wannan aiki na Sadakatul-Jarriya a bude take.
Ga duk wanda ke son bayar da gudunmuwansa yai amfani da wannan kafa ne kawai domin haka.
Ta asusun da aka bude;
Lamban Account:- 5601116694
Sunan Account:- ZAZZAU MOSQUE ENDOWMENT
Sunan Banki:- FIDELITY BANK PLC
Da fatan Allah Ya ba da ikon taimakawa.
Sa Hannu:- ABDULLAHI ALIYU KWARBAI,
Mai Magana Da Yawun Masarautar, Zazzau

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here