Home Lafiya Tsananin zafin rana: Hukumomin Kano sun Bayar da shawarwari don kauce wa...

Tsananin zafin rana: Hukumomin Kano sun Bayar da shawarwari don kauce wa kamuwa da cutuka

109
0

Hukumar kula da asibitocin Kano ta shawarci al’ummar jihar su gaggauta ziyartar asibiti mafi kusa da su da zarar sun ji wasu alamu na rashin lafiya a jikinsu.

Sakataren hukumar, Dr Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Samira Suleiman ta sanya wa hannu.

Dakta Mansur Mudi Nagoda,ya bayar da shawarar ne don kauce wa cutar ƙyanda da wata cuta da ake samu sakamakon tsananin zafi da jihar ke fuskanta

Sanarwar ta ce alamomin cutukan sun haɗa da zazzaɓi mai tsanani da ciwon kai da amai da ciwon wuya da bushewar maƙogoro da kasala da sauran alkamomi.

Dakta Mansur Mudi Nagoda ya ce za a samar da tawagar gaggawa ta musamman da za ta riƙa kula da marasa lafiya a asibitocin jihar.

Sanarwar ta kuma ce mutanen da ke fama da cutar siga da hawan jini su nemi shawarar likitoci a wannan lokaci da ake fama da tsananin zafi.

Shugaban hukumar ya kuma shawaraci mutane su yawaita shan ruwa tare da guje wa yawo a cikin rana, da kauce wa kwanciya a ɗakunan da ke cike da cunkoso.

Birnin Kano da wasu yankunan arewacin Najeriya na fama da tsananin zafi, lamarin da ake fargabar ɓarkewar cutukan da ke da alaƙa da zafin.(BBC)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here