Home Labaru masu ratsa Zuciya Hadarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 5 A Garin Naira dake...

Hadarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 5 A Garin Naira dake Jihar Kano

384
0

A kalla  mutum biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon tawo mu gama da wasu motoci biyu sukayi a kauyen Naira dake karamar Hukumar Gezawa dake Jihar Kano da safiyar yau Juma’a.

Wakilin Viewfinder wanda ya isa wurin hadarin yan mintina kadan da faruwar ya rawaito mana cewa hadarin ya faru ne a sakamakon barchi da ya kwashe  direban motar Haice wacce ake yiwa lakabi da Homa.

Wasu daga cikin wadanda abun ya faru a gabansu sunce motar Homa taci karo ne da wata kurkurar mota wacce take dauke da shanu wacce ta lalace a bakin hanya.  Sunce ana cikin gyaran kurkurar ne ita wannan mota ta Haice (Homa) ta kufce ta bugi kurkurar .

Lokacin da wakilin mu ya halarci wurin babu wani jami’in dan sanda ko na hukumar kare haddura da ya isa wurin amma mutanen dake wurin sunce an bugawa yan sandan Gezawa waya amma basu iso wurin ba.

Daya daga cikin fasinjojin mai suna Usman wanda ke zaune a gaban motar yace bai san yadda hadarin ya faru ba shi dai ya gansu kawai cikin jini. Shima Direban motar yace shima bai san yadda abun ya faru ba.

Usman ya sanar damu cewa mutanen Jigawa ne a cikin motar Homa wadanda suke kan hanyarsu ta komawa gida hutun karshen shekara daga Jihar Enugu kuma motar tasu garin Hadejia ta nufa.

Daga cikin mutane goma sha biyu da suke cikin motar mutum biyar sun mutu nan take sauran kuma sun tsira da munanan raunuka.

Suma masu kurkura sun sami raunuka a inda shanun da suka dauko suma sun sami rauni a inda motocin dukansu sun fita daga haiya cinsu.

Wakilin Viewfinder ya yi kokarin tuntubar lambobin gaggauwa na jihar Kano domin sanar dasu faruwar hadarin amma wasu layukan sun shiga ba’a dauka ba wasu kuma basu shiga ba ma

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here