Home Siyasa Zaben 2023 Manuniya Ce Ta Kawo Canji A Shugabancin Najeriya – Inji...

Zaben 2023 Manuniya Ce Ta Kawo Canji A Shugabancin Najeriya – Inji Hon. Gumi

237
0
Hon. Gumi

An baiyana zaben shekara ta 2023 a wani mataki na kawo gyara akan shugabanci da siyasar Najeriya.

Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Gumi/ Bukuyum da ga Jihar Zamfara Hon. Sulaimain Abubakar Gumi ne ya baiyana haka a hirarsa da Yan Jaridu a ofishin sa da ke Abuja.

Hon. Gumi wanda ya bayar da misali da Majalisar Taraiya to 10 da cewa tasha bambam da sauran Majalisu da suka gabata idan aka duba irin wakilcin da ta samar da ga jam’iyu dabam-dabam.

“idan ku ka duba majalisa ta 10 za ku yarda dani cewa mutane sun fara wayewa a siyasar Najeriya na zabo mutane daga jam’iyu dabam-dabam. Akwai yan AFGA, NNPP, APC, PDP da LP sauran Jam’iyu . Hakan ya sabawa yadda ake yi a baya na zabar Jam’iyu guda biyu kawai”.

Ya ce hakan na nufin mutane sun fara zabar cancanta ba tare da la’akari da jam’iyar da mutum ya fito ba. Sabo da haka, idan shugabanci bai gyaru daga sama ba mutane zasu gyara shugabanci da ga kasa ta hanyar zaben cancanta. Sabo da haka dole wanda aka zaba yayi abun da jama’arsa suke so ko kuma su canza shi a wani zaben mai zuwa.

Hon. Gumi ya kara da cewa batum Najeriya cika shekaru 63 da samun yancin kai kuwa har yanzu muna tafiyar wahainiya idan aka kwatanta da sauran kasashe da muka samu yanci tare.

“Babbar tambayar anan it ace, har yanzu kasashen Africa sun sami yanci?. Yace kasashen Africa musamman wadanda kasar Faransa ta mulka suna karkashin mulkinta sai yanzu da suka fara bujurewa ta hanyar yin Juyin mulki, koda ya ke ba abu mai kyau bane, amma sun fara fahimtar irin zaluntar su da ake yi.

Gumi ya ce babban matsalar Najeriya itace rashin shugabanci  na gari, inda ya bada misali da kasar Dubai wacce ya ce shugaban kasar ne ya kawo canji ta hanyar yin aikace-aikace da suka canja kasar. “ A halin yanzu idan za’a saka kasashe da sukaci gaba a duniya dole a saka Dubai.

Ya ce abun takaici ne, ace har yanzu Najeriya bata da Jiragen sama na ta, kasar da abaya har kyautar jirgin sama takeyi. Yanzu kasar Saudi Arebia jiragen da take da su basu da iyaka, kasar da a baya sai ta nemi taimakon Najeriya da ta ba ta Jirage domin ta kwashi alhazai.

Hon. Gumi,  ya ce har yanzu matsalar Africa itace ta rashin shugabanci na gari, sabo da haka idan an sami shugabanni na gari Najeriya za ta cigaba kamar kowacce kasa a Duniya domin Allah ya bama dukkan abubuwan da muke bukata kamar yawan jama’a da ma’adanai da yalwatacciyar kasa mai albarka da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here