Home Mai da Iskar Gas Duk Da Ikirarin NNPCL: ‘Har Yanzu Matatar Fatakwal Ba Ta Fara Fitar...

Duk Da Ikirarin NNPCL: ‘Har Yanzu Matatar Fatakwal Ba Ta Fara Fitar Da Man Fetur Ba’

3
0
Matatar Fatakwal

Masu hada-hadar man fetur a Najeriya na kokawa kan yadda suke samun matsala wajen samun fetur daga matatun gwamnati guda biyu da aka gyara kwanan nan—matatar Fatakwal da na Warri—shekara daya bayan da aka bayyana cewa sun fara aiki.

 

Najeriya, wadda ta shafe shekaru tana fama da ƙarancin man fetur, ta kashe kimanin dala biliyan 2.4 tun daga shekara 2021 domin farfaɗo da waɗannan matatun da ke yankin Niger Delta, da nufin dakatar da dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje. Sai dai har yanzu, ba su fara fitar da man fetur ba.

 

Kungiyar ‘yan kasuwa masu gidajen mai ta Najeriya, PETROAN, ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa sama da mambobinta 6,700 har yanzu na dogaro da shigo da mai daga waje da kuma matatar Dangote.

 

Bisa bayanan ƙungiyar, har zuwa watan Maris babu wani fetur da aka fara fitarwa daga matatar Fatakwal wadda a da ita ce mafi girma a kasar.

 

A cikin wannan watar dai, matatar Dangote ta samar da lita miliyan 20.6 na fetur, yayin da aka shigo da ƙarin lita miliyan 25.19 daga waje—wanda duka ya kai kashi 92 cikin 100 na buƙatar lita miliyan 50 da ake bukata kullum a Najeriya.

 

Matatar Fatakwal dai na ci gaba da tace danyen mai don samar da dizel.

 

Kamfanin NNPC, wanda ke gudanar da matatun Fatakwal da Warri, bai mayar da martani ba kan dalilin da yasa ba a fara fitar da man fetur ba

 

Kungiyar PETROAN ta buƙaci a bayyana gaskiya game da halin da matatun ke ciki, tana mai cewa: “’Yan Najeriya na son sanin taƙamaiman ranar da za a kammala aikin gyaran matatun.” (BBC Hausa).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here