Home Siyasa Ziyarar Buhari Kano: PDP da APC na ta cece-kuce akan abin da...

Ziyarar Buhari Kano: PDP da APC na ta cece-kuce akan abin da ya faru

206
0

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da babbar jam’iyyar adawa ta PDP na musayar kalamai kan abubuwan da suka faru a lokacin ziyarar shugaba Muhammadu Buhari zuwa jihar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan wasu hotuna da aka yaɗa a shafukan sada zumunta, inda ake cewa wasu ne suka yi jefe-jefe a lokacin ziyarar ta shugaban ƙasa domin nuna adawa.

Sai dai jam’iyyar All Progressive Congress ta musanata labaran da ke cewa an kai wa ayarin shugaban na Najeriya hari a lokacin ziyarar ta jihar Kano.

Inda ta ƙara da cewa bayanin da ke cewa an jefi shugaba Buhari wani ƙagaggen labari ne da jam’iyyar Peoples Democratic Party ta ƙirƙira domin zubar da ƙimar shugaban ƙasar.

Tun farko mai magana da yawun kwamitin zaɓen shuigaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye ya wallafa bidiyon da ke iƙirarin cewa an jefi tawagar shugaba Buhari a lokacin ziyarar ta Kano.

Haka nan jam’iyyar PDP, a wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun sakataren yaɗa labarunta na ƙasa Hon Debo Ologunagba, ta yi Alla-wadai da abin da ta kira hari kan tawagar shugaban ƙasar.

Inda ta bayyana harin a matsayin wani yunƙuri na yin zagon ƙasa ga fadar shugaban ƙasa, da tayar da husuma, da kuma yin cikas ga babban zaɓen ƙasar na 2023.

Sai dai sanarwar ta ƙara da cewa “babban abin damuwar shi ne yadda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ke ƙoƙarin illata da kuma kunyata shugaba Buhari a lokacin da yake gudanar da aikinsa.”

Sai dai a wani martani da jam’iyyar APC ta mayar ta hannun daraktan yaɗa labaran kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ta zargi PDP da kitsa batun jifar shugaban ƙasar.

Sanarwar ta ce “batun kai hari a kan tawagar shugaba Buhari wani hasashe ne kawai na sakataren yaɗa labarun jam’iyyar PDP na ƙasa.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “kamar yadda PDP take ƙirƙirar ƙarya a kan ɗan takaran shugaban ƙasa na APC domin haifar da rikici, muna da imanin cewar PDP ɗin ta kitsa wani yunƙuri na kunyata shugaba Buhari a lokacin ziyarar ta jihar Kano domin ta ɗora laifi kan gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu.”

Kuma sanarwar ta buƙaci al’ummar Najeriya su yi watsi da bayanan da suka fito daga jam’iyyar PDP, tare da bayyana su a matsayin marasa tushe. (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here