Home Siyasa Zargin Cushe A Kasafin Kudin 2024: Ba Ma Yin Abubuwa Kamar Dattawa...

Zargin Cushe A Kasafin Kudin 2024: Ba Ma Yin Abubuwa Kamar Dattawa Ne Dalili – Inji Sanata Ndume

156
0
Sen. Ndume 2

Mataimakin Shugaban Kasafin Kudi na Majalisar Datttawa Sanata Ali Ndume ya ce cecekuce da a ka yi a Majalisar Datttawa jiya Talata akan zargin da ake yiwa Sanata Abdul Ningi na kage ya farune sabo da Yan Majalisar basa yin abubuwa kamar Datttawa.

Ya ce yarda Yan Majalisar Wakilai su ke gudanar da al’amuran su abun sha’awa ne duk da yake a bangaren su ne ya kamata  a rinka samun hatsaniya sabo da dalili na yarinta da jini a jika amma sai a Majalisar Datttawa a ke samun kace  nace sabo da basayin abubuwa kamar Datttawa.
” Ai Majalisar Datttawa tana bukatar gyara ko kintsuwa. Ga Yan Majalisar Wakilai  nan shiru ka ke ji.  To su ne masu sabon jini ba sa yarinta amma kuma mu  mun koma mu na yarinta. To ka ga akwai matsala. Laifin na mu ne duka domin ba ma tsayawa mu yi abu kamar yadda Datttawa ya kamata su yi. Wannan abun da Abdul Ningi ya yi da bai faru ba”.
Sanata Ndume ya cigaba da cewa,  abun kunya ne ace an yiwa Arewa koro a cikin Kasafin Kudin na 2024 domin yadda Yan Arewa su ke da ruwa da tsaki a cikin kasafin kudin. In da ya ce Shugaban Majalisar Wakilai Dan Arewa ne, Shugaban Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai Dan Arewa ne. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa,  Dan Arewa ne ,Mataimakin Shugaban Kasafin Kudi,  wato ni ke nan Dan Arewa ne . Ministan Kasafin Kudi,  Atiku Bagudu Dan Arewa ne. Ta ya ya za a ce anyi Kasafin Kudi an cuci Arewa.  Kai kasan hakan ba zai yiwu ba. Inji shi.
Ndume ya ce kasafin kudin ya samu amincewar Yan Majalisar domin kuwi Abdul Ningi da Kawu Sumaila da sauran yan Arewa su na gurin aka amince da kasafin kudin daya bayan daya amma basu ce an cuci Arewa ba, sai yanzu duk da cewa Kasafin Kudin yana hannun su tsawon wata guda kafin a amince da shi.
Ya kara  da cewa Abdul Ningi ya yi kuskure domin ya kamata a ce ya sanar da Sanatocin Arewa wuraren da ya ke zargin an yi ba daidai ba domin su tabbatar amma bai yi hakan ba.
” ya ajiye bayanai ga kan sa shi kadai, ta yaya zan goyi bayan abun da ban sani ba”.
Sanata Ali Ndume ya yi karin haske akan kudade da ake takaddama akan su na sama da Naira Tiriliyan uku, wanda ya ce kudade ne da ake bawa wasu ma’aikatun da ba a sa su acikin rahoton kasafin kudin kamar su Ma’aikatar Shari’ah da Majalisar Taraiya da  Hukumar Zabe ta Kasa da TETFUND da sauran su.
Yace wadannan kudade idan aka hada su da Tiriliyan 25 su ne su ka bayar da sama da Naira Tiriliyan 28 da Majalisar Taraiya ta amince da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here