Home Tsaro ‘Zamu yi aiki ba dare ba rana domin ganin an yi zaben...

‘Zamu yi aiki ba dare ba rana domin ganin an yi zaben gwamnoni lami lafiya a Najeriya’

209
0

Hukumomin tsaro a Najeriya, sun ba da tabbacin cewa za su yi aiki ba dare ba rana don ganin an yi zaɓukan gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi lafiya a ƙasar.

Babban mashawarcin tsaro na ƙasar, Janar Babagana Monguno, mai ritaya ne ya bayyana haka lokacin wani taron kwamitin tuntuɓa tsakanin hukumomin tsaro kan sha’anin zaɓe a kasar.

Janar Babagana Monguno, ya ce zaben gwamnoni da na ‘yan majlisun jihohi na da sarkakkiya.

Ya ce, “ Zabukan gwamnonin sun sha bamban da na shugaban kasa don kuwa zabe ne guda 1,02, abin da ke nufin za a samu karin mutanen da za fita don kada kuri’a.”

Babban mashawarcin tsaron ya ce za kuma a samu karin cibiyoyin tattara sakamakon zabe.

A don haka, Janar Babagana Monguno, ya ce yana magana da babban hafsan tsaro da kuma babban sifetan ‘yan sanda na Najeriya wadanda ke jagorantar tsare tsaren zaben gwamnonin da ke tafe.

Babban mashawarcin ya ce, dole ne jami’an tsaro su yi aiki bisa doka sannan su bar duk wanda ya cancanta ya kada kuri’arsa.

Janar Babagana Monguno, ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa su gargaɗi magoya bayansu a kan su guji tada hankula a lokacin zaɓukan gwamnonin da ke tafe.

A bangare guda kuma, rundunar ‘yan sandan Najeriyar ma ta ce, ta tura ƙarin ma’aikata da kayan aiki don ƙarfafa matakan tsaro lokacin zaɓen gwamnoni mai zuwa.

Rundunar ta kuma ce a baya-bayan nan, jami’anta sun ƙwato miyagun makamai 182 daga hannun mutanen da ake zargi sun mallake su ba bisa ƙa’ida ba. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here