Home Mai da Iskar Gas Zamu Tabbatar An Hukunta Duk Wadanda Su Ka Shigo Da Gurbataccen Mai...

Zamu Tabbatar An Hukunta Duk Wadanda Su Ka Shigo Da Gurbataccen Mai Kasarnan, Kawo Cikas Ga Matatar Mai Ta Dangote – Sanata Wadada

95
0
Dangote refinery

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Nasarawa ta Yamma  Sanata Aliyu Wadada ya ce Majalisar Taraiya ba zata zu ba ido ba ta ga wasu mutane a kasarnan ko su wanene su ka shigo da gurbataccen Mai da yunkurin kawo cikas ga matatar Mai ta Aliko Dangote da ke kokarin kawowa Yan Najeriya sauki na rayuwa.

Dan Majalisar ya baiyana haka ne ga Yan Jaridu jimkadan da kammala zaman majalisar na jiya Laraba yadda majalisar ta gudanar da zazzafar mahawara akan kuduri na gaggawa da aka gabatar akan shigo da gurbataccen Mai da aka yi kasarnan wanda hakan ya fusata dukkanin Yan Majalisar.

Yan Majalisar sun soke dukkan jadawalin gudanarwa su na Majalisar na wannan rana domin tattaunawa akan illar da ake yiwa Kasarnan a bangaren Mai wanda shi ne kashin bayan tattalin arzikin Kasarnan.

Sanata Wadada wanda na da ga cikin Sanatocin da su ka nu na fushin su da takaicin abun da ya ke faruwa a Kamfanin Mai na Kasa wato NNPCL wanda shi ne kadai ke da alhakin shigo da Mai Kasarnan.

Sanata Wadada Kifi

Bayan da aka kammala zazzafar Mahawarar Majaisar ta shiga zama na sirri wanda ta Kafa wani Kwamiti wanda zai binciki yadda aka shigo da gurbataccen Mai a Kasarnan.

Wadada ya ce ba zata sabu ba, bindiga a ruwa, tun da Majalisar ta yi Doka wacce aka amince da ita na gudanar da Kamfanin NNPCL a matsayin mai zaman kansa amma tunda aka kafa kamfanin ya gaza kawo wa Kasarnan kudaden shiga da ake saka rai.

Sanatan ya kara da cewa a bangaren Kamfanin tace Mai na Aliko Dangote wa su mutane su na yunkurin kawo masa cikas na gudanar da kamfanin nasa na hana shi danyen Mai domin ya tace; sai ya je wasu kasashen duniya sannan ya shigo da Mai da zai tace.

Sabo da haka, Sanata Wadada ya ce Yan Majalisar ta 10 sun sha alwashin hukunta duk wanda su ka samu da hannu wajen shigo da gurbataccen Mai Kasarnan da yunkuri na kawo cikas ga Matatar Dangote.

Sanata Wadada ya yiwa Yan Najeriya alkawarin cewa za su gudanar da binciken su ba sani ba sabo kuma duk wanda su ka samu da laifi za su baiyanawa Yan Najeriya shi kuma za su saka ido su ga an hukunta su.

A nasa gudunmawar, Sanata Sani Musa ya bayar da shawarar ganin an sake yin gyara a kan Dokar PIA wacce ta bawa Kamfanin NNPCL karfi da yawa wajen gudanar da kamfanin.

Shima Sanata Ali Ndume wanda ya karawa Yanjaridu haske, ya goyi bayan ganin an gyara Dokar tare da bincikar wadanda su ke so su kawo cikas ga Kamfanin Mai na NNPC da Matatar Mai ta Aliko Dangote.

Y ace sun hana Matatun Mai na NNPCL aiki sannan kuma sun a yunkurin ganin sun kawowa Matatar Mai ta Dangote Cikas wanda kishin Kasa ta shay a zuba dukiyar sa wajen ganin ya kawowa Kasarnan mafita sakamakon gazawa ta Kamfanin NNPCL amma kuma wasu sun a yunkurin kawo masa cikas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here